Ya na dauke da sinadarin ‘dimeric flavonoid’
A na noman wannan dan itace ne a kasashen Najeriya, da Kamaru, da Ghana, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Benin, da Kwadebuwa, da Gabon, da Saliyo, da Laberiya, da kuma Sanegal. Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin namijin goro ga lafiya.
A tarihance, likitoci a Afirka sun yi imani cewa, namijin goro na da sinadarin yakar kaska, da yashe ciki, da kuma yakar kananan kwayoyin cuta. Da farko dai likitoci na amfani da shi don maganin tari da cututtukan makogwaro, da bututun iska, da ciwon kai ko sanyin kirji, da kuma ciwon ciki. Bugu da kari, tsarin maganin gargajiya na Afirka ya nuna masu matsalar hanta ka iya tauna namijin goro.
Wannan dan itace na taimaka wa wajen maganin dukkan nau’i na tari, a na kuma amfani da shi wajen maganin sanyi.Yawanci kuma ya fi amfani wajen kakkabe mashako, da tari, da toshewar hanci, da kuma majina. Namijin goro ya na taimakawa wajen yakar miyagun cututtuka kamar Ebola, ya na kuam dauke da sinadaran yakar dadewar fata da sauransu. Ya na kara karfin kwaranyar jini ga mutanen da ke da matsala da bututun da ke dauko jini daga zuciya. Sannan ya na taimaka wa garkuwar jiki,domin binciken kimayya na musamman ya tabbatar da cewa, yawan amfani da shi na ba da kariya ga garkuwar jikin dan adam. Har ila yau Namijin goro na warkar da ciwon gwiwa wajen rage mata radadi sosai yana kuma amfani wajen jin yunwa sannan ya na sa jin kishirwa.
The post AMFANIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR KA/ KO KE appeared first on MUJALLARMU.