Maryam Musa Waziri na daya daga cikin jarumai na sabon Fim da Kamfanin Aminu Saira zai fito dashi mai suna Labarina. Labarina ya kasance Fim na Series na Farko da za’ayi a Kannywood. Sannan kuma tayi wani sabon Fim mai suna Muguwar Mace wanda shima har yanzu bai fito ba.
Maryam Musa Waziri wadda akafi sani da MaryamWazeery yar Jahar Gombe ce, Kuma ta fara Fim ne domin tana Sha’awar Fim sannan kuma tana so Ilimantarwa ta hanyar Nishadi.
A tattaunawarta da Mujallarmu ta bayyana cewa Aminu Saira ne babban abun Koyi da Shawarta a wajenta.
Ta bayyana cewa zata so taga tayi tasiri wajen taimakawa Ilimantarda Al’ummah ta hanyar Nishadi.
The post ABUNDA YA KAMATA MUSANI AKAN SABUWAR JARUMAR FIM DIN LABARINA appeared first on MUJALLARMU.