Kafin kowa yai tambaya idan haka yake kafin munyi aure, toh ansar ita ce: ba haka yake ba. Bai taba fada min bakaken kalamai ba ko muna biyu bale ma cikin jama’a. Amma abun mamaki shine, tun farkon auren mu yake musguna min gaban Kannen shi.
Ya ci mun fuska a gaban mai aikin famfo saboda na ce masa farashin kayan da za’a saya yayi yawa. Sa’an nan ma a gaban mai aiki Ya aikata ya fi a kirga. To har ya kai ga yar aikin bata jin magana ta domin ya fada mata idan na sata aiki kada tayi.
Wani abu da bai sani ba shine, wannan abu da yake aikatawa na rage son da nake mishi, saboda ba amfanin son mutun min da baya ganin girmanka. A lokacin baya inajin dadin bayyana ma mutane irin son da nake mishi amma yanzu kam kokadan bazan iya yabon shi ba.
Wannan yana sa min damuwa sossai dan gaskiya na fara tunanin ramawa nan gaba idan ya ci min fuska gaban Mutane saboda yaji irin abun da nake ji, saboda bai taba bani hakuri ko yaji bai kyauta ba akan abun da yakeyi ba. Kullun maganar sa shine shi baya boye abu a zuciyar shi. ni kuma na tambaye shi “koda abun zai bata wa Matar ka rai”.
Abun na damuna saboda zamuyi tafiya kwanan nan zuwa gida, kuma ina tsoron idan ya ci mun fuska gaban Yan uwa zan iya ramawa idan raina ya bace sossai.
Dan Allah ina so a bani shawara ta gari saboda ban so in saka wani a cikin wannan Matsalar.
The post LABARINA: MIJINA NA CIMUN FUSKA A IDON JAMA’A appeared first on MUJALLARMU.