Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

NASIHA

$
0
0

Mutum da Mutum ƴan uwan juna ne tun azal, ba wai sai an haife su gida ɗaya ba. Kuma ko wane ɗan uwa dole za ka sa me shi yana son ɗan uwansa, a koda yaushe yana kula da shi idan shi ne ke kan gaba, shi kuma wanda ake kan gaban shi yana nuna biyayyarsa ga wanda yake gaba da shi. Idan kuma aka sami akasin haka daga gefe ɗaya, to lalle wanda aka samu giɓi daga gefensa yana da matsala ta jahilci duniyance da addinance ko ƙaramcin wayewa. Ba lalle ba ne, wanda ya fi girman shekaru shi ne zai taimakawa ƙarami ba, ko wanda ke da tarin dukiya zai taimakawa talaka ba, sai dai wanda duk yake da abin taimakawar da wani ɗan uwansa ke buƙatuwa da shi, to shi ne haƙƙi ya rataya kansa ya taimaka. Kuma yin taimako shi ne kawai zai sa mutum ya kasance mai sauke wajibin da yake kansa a cikin al’umma. Idan ya kasa aikata haka, to ya zama tamkar Juji (Shara) a cikin mutane. A taƙaice dai, a iya cewa yaro zai iya amfanar da babba, kamar yadda talakka zai iya amfanar da mai kuɗi. Jahili yana buƙatar taimakon mai ilmi, talakawa da shuwagabanni na buƙatar taimakon junansu da na masu arziki a cikinsu. Kamar dai yadda aka san duka ɗan Adam ba zai rasa inda yake da naƙasi ba, yake kuma buƙatuwa da taimakon wani a inda ya ka sa ɗin. Duk dai yadda ta kasance, idan mutum yana jin ƙishirwar da ba ya da ikon gusar da ita sai tare da taimakonka, wajibi ne kaba shi ruwa yasha, idan girman kai ya hana mai ya karɓa daga gare ka, to yanzu kuma kyautatawa ce idan ka lallaɓe shi, ka fahimtar da shi, kana lurar da shi akan hatsarin da ke cikin rashin shan ruwan nan nan. Daga nan idan ya ƙi karɓa har ya halaka, shikenan, ya halakar da kansa kenan. Kai ka yi abinda ake buƙatar kayi, ka kyautata a fuskar addini da kuma ta zamani. To sai dai kuma in za ka bayar da taimako, idan gida na so, ai bai dace akai daji ba. Mutumen da yake mance wa da mafarinsa kuma ba abin yabo ba ne. Misali, Idan mutum ya bar gidansa da ƙazanta, sai ya je yana share hanya yana tsaftace ta don mutane suji daɗin wucewa, ina ganin sunansa mahaukaci ba mai taimako ba. Kamar dai yadda ɗimbin mutanen ƙauye da ke zaune a birni suka mance da ƙauyukansu. Yanda tsan-tsar Jahilci na addini da zamani ya yi wa wasu ƙauyuka yawa abin haushi ne, inda har ta kai za ka ga saurayi ɗan shekara 25 zuwa 30 bai iya karanta Fatiha ba, ko ma tsoho ɗan shekara saba’in zuwa sama. Abin mamaki kuma sai kaji ance Dr. Ko Farfesa Wane daga ƙauyen nan ya fito, ko kuma Malam wane ko Honourable ko Alhaji wane ai ɗan kauye kaza ne. Lokaci da yawa idan na tuna da Sani Sabulu a inda yake cewa “Ni Sani sabulun Haja, Ni na Amina ƙanen Inno, A cikin sana’ar waƙa, ban san ƙauye da ƙauna ba, Tafiya ƙasa ba ta hana min, in je ƙauye da Gangata, Bani mance mutanen ƙauye, don na san jama’ar birni, Bani rena mutanen ƙauye, wai don na san jama’ar birni, Kauye an ka yi yaye na,…. kauye an ka yi min aure, sannan nissan jama’ar birni….” sai in yaba mai sosai, kuma in jinjina wa tunaninsa, a daidai yadda nake ganin kasawar waɗanda suka zo birni suka manta da ƙauye. So da yawa kuma sai in rasa gane wa ye mai laifi a cikin wannan lamari. Ko shakka babu na tabbatar jama’ar da ke zaune a ƙauyuka, suna buƙatar taimakon jama’ar da ke birni ta ɓangarori da dama. Ƙauye ba su da ruwan sha na ƙwarai, ba su da wutar lantarki, ba su da motocin hawa na jin daɗi, ƙauye ba su da ilmin addini wadatacce ballai na zamani. Abin da ban gane ba shi ne: Shin ƴan ƙauye ne da suka dawo birni suka zama wata tsiya, kamar gwamnoni, kwamishinoni, ministoci da wasu ƴan majalisunmu ya fi can-canta su rinƙa kai wa ƙauyuka ɗauki? Ko kuma ire-irenmu waɗanda tun kaka da kakanni hulɗarmu da ƙauye ta yanke? A tawa fahimtar, ƙauyuka ne suka haifi birane. Don haka duk ƴan birni asalinsu ƙauye ne, ashe ko ya zama dole mutum ya kula da asalinsa in dai ga hankali da sanin ya kamata. Bai kamata mubar mutanen ƙauye a matsayin wasu bayin da ke noma muna hatsi da shinkafa muna ci ba, wannan ba adalci ba ne. Koda ko ba ƴan’uwanmu na zumunta ba ne a can, to lalle ƴan’uwanmu ne a addini, inba a nan ba, to tabbas ƴan’uwanmu ne na kasancewar mu duka ƴan Adam. Kuma dukan mu muna da gudunmawar da za mu iya ba su. A ƙauyuka ne fa za ka samu mata ma’aurata, ba su da aikin da ya wuce zuwa rafi ɗebo ruwa. Idan sun dawo gida, sussukar hatsi sai daka, shine kawai aikin. Babu ilmin addini ballai na boko, don haka sallar ma koda ana yi, ana yin ta ne don tana da wani matsayi a cikin jerin ayukan yini, amma ba don an san muhimmancin ta ba. Mafi yawan budare mata a ƙauye, idan bayan zuwa gona da rwahi, da idan dare ya yi aje wurin gaɗa a dan-dali ba su san komai ba. Basu ma san idan an yi aure an rayar da sunnar Annabin Allah ba ne, suna yi wa abin wata fahimta ne ta daban. Ba waɗannan ne kawai matsalolin ƙauyukanmu ba, amma dai mu tsaya a nan. Fatar da nake dai, Allah Ya sa wannan tsoakci ya amfane mu, kuma ya sanya mu cikin wadanda za su taimaki al’ummar da ke buqatar taimako, ba mu yi ta vata gashiri gurin dahuwar qaho ba. Ameen Yabo da godiya sun tabbata ga Allah

The post NASIHA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>