Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all 3050 articles
Browse latest View live

ABUN AL’KAIRI DA YA FARU DA BUKOLA SARAKI A JAHAR ZAMFARA kukaran ta

$
0
0

Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Abubakar Bukola Saraki a matsayin Dan Iyan Kauran Namoda jiya. a kwanaki ne kuma aka na da Turakin Ilorin din a matsayin Baban Addini. Wannan ya faru ne lokacin da shugaban Majalisar ya isa Jihar Zamfara domin daurin auren ‘ya ‘yan Sanata Tijjani Kaura da aka yi a fadar Sarkin Kauran Namoda. Alhaji Muhammad Asha ya nada Bukola Saraki inda yace ya cancanta.

 

The post ABUN AL’KAIRI DA YA FARU DA BUKOLA SARAKI A JAHAR ZAMFARA kukaran ta appeared first on MUJALLARMU.


labarai da dumi dumin ta BAKIN CIKIN YAN NAJERIYA ZAI HALLAKA SU SHINKAFA YA SAUKO

$
0
0

yanzu haka an fara saida buhun shinkafa a kan kudi N11, 000 a Garin Kaduna. Farashin buhun shinkafa dai ya fi haka tsada tun bayan da ake shigowa da ita cikin kasar. Wata kungiya mai zaman kan ta ce dai ta ke saida wannan shinkafa araha banza kan N11, 000 yayin da ake saida na kasuwa kan kusan N17, 000. Wasu ‘yan kasuwar dai sun kai kara wajen ‘yan sanda inda su kace ana saida buhu kasa da ainihin farashin sa

Tun ranar Litinin dai aka fara saida wannan shinkafa a daidai layin nan na Gamagira a Kasuwar barci da ke cikin Garin Kaduna. Mutane da dama dai sun taru domin samun na su buhun da wani dan kasuwa mai suna Sudais yake saidawa. Kwanaki wani Darekta a Ma’aikatar yada labarai na Najeriya ya rubuta wasika ga Hukumar kwastam ta kasa inda yake bayyana mata cewa wasu na cigaba da shigo da shinkafa makare a boye cikin kasar.

The post labarai da dumi dumin ta BAKIN CIKIN YAN NAJERIYA ZAI HALLAKA SU SHINKAFA YA SAUKO appeared first on MUJALLARMU.

YANZU YANZU WANI DAN MAJALISSA YA RASU- MA’ANA YA MUTU

$
0
0

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa wani dan majalisar ya tafi lahira a safiyar yau, Lahadi, 23 ga watan Afrilu.

Adeleke  Ya ci zaben Sanatan jihar Osun a karkashin dandalin All Progressives Congress (APC) a 2015, kamar yadda mujallarmu ta samu rahoton. Majiyar marigayi na bayyana wanda ya rasu sakamakon ciwon zuciyar bayan an garzaya da shi zuwa Asibitin Bikets. A can ne ya mutu.

Adeleke ne Sanata daga yankin Osun ta yamma a majalisar dattawan kasa. Ya rasu mai shekaru 62. Allah ya jikansa domin musulmi ne

The post YANZU YANZU WANI DAN MAJALISSA YA RASU- MA’ANA YA MUTU appeared first on MUJALLARMU.

SAKO ZUWA GA MATAN AURE

$
0
0

Ya kamata duk matar da ta tsinci kanta adakin aure, awannan zamanin da muke ciki, ta gode ma Allah. Ba don komai ba, idan ta duba zata ga wasu ‘yan-mata irinta, sunfi ta kyawun halitta da iya ado, amma har yanzu basu samu mijin aure ba.

Don haka zai fi alkhairi agareki ki Qudurce acikin zuciyarki cewa GIDAN MIJINKI NAN NE WAJEN NEMAN ALJANNARKI.

Ki rike mijinki hannu bibbiyu, ki kula da tsaftar jikinki da tsaftar Muhallinku. Kuma ki zama ko yaushe ashirye kike domin biyan bukatar mijinki ko da bai nema ba.

Ki kiyaye MUGAYEN QAWAYE… Ba zasu rasa yi miki hassada ba. Tunda ke kin samu miji, su kuwa basu samu ba… Dole suyi miki hassada.

Ki kiyaye sirrin mijinki, kar ki gaya ma kowa.. Musamman ma kawayenki zasu so suji abinda yake faruwa.. Don haka kar ki gaya musu.

Idan kuna da ‘ya’ya to ki kula dasu, ki kula da tsaftarsu. in ma ‘ya’yan kishiyarki ne, to ki kula dasu kamar yadda zaki kula da ‘ya’yanki.

Ki kiyaye dukkan amanonin mijinki. musamman ma iyayensa da ‘yan uwansa da dukiyarsa.

The post SAKO ZUWA GA MATAN AURE appeared first on MUJALLARMU.

BANBANCIN MANIYI DA MAZIYYI NA MATA DA NA MAZA

$
0
0

Muna yawan samun tambayoyi akan wannan Matsalar daga bangarorin Maza da mata. Amma in sha Allahu yanzu zanyi bayani daidai gwargwadon iko.

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Ina fatan zaku gafarceni. Zanyi bayani dalla dalla (duk da cewar akwai nauyi sosai) to amma abu ne wanda ya shafi addini. Kuma bangaren tsarki ne wanda sai dashi ibadah zata yiwu.

Maniyyi da Maziyyi suna da bambanci ta bangarori guda uku kamar haka:

1. Bambanci a yanayin Siffarsu.

2. Bambanci ayanayin da ake ji bayan fitarsu.

3. Bambanci a bangaren hukuncinsu.

1. SIFFOFINSU
*****************
Manzon Allah (saww) shi da kansa yayi bayanin yadda siffarsu take yayin da yake bada amsa bisa tambayar da Sayyidah Ummu Sulaym tayi masa.

Yace : “SHI DAI MANIYYIN NAMIJI, FARI NE KUMA YANA DA KAURI. SHI KUMA MANIYYIN MACE, FATSI FATSI NE, KUMA TSINKAKKE NE (BASHI DA KAURI).

(Bukhary da Muslim ne suka ruwaitoshi).

Akan wannan ne malamai sukayi Qarin bayani cewa Shi maniyyin Namiji yana Qamshin Furen dabino ne. Kuma yana fita ne tare da zunkudar junansa. (wato yana fita da Qarfi). Shima na macen haka yake.

Kuma in dai maniyyi ya fita daga Mace ko Namiji, acikin barci ko afarke, to yana Wajabta wanka.

Sai dai wadanda suke tare da Larura ko jinya, ko kuma ta dalilin faduwa daga sama, har maniyyi yakan fita daga garesu ba tare da motsuwar sha’awar komai ba, to wannan ba ya karya azumi kuma ba ya wajabta wanka.

Shi kuma MAZIYYI duk kala daya ne na mata da na Mazan. fari ne shi garai garai. Kuma yana fitowa ne bisa dalilin motsawar sha’awar Jima’i. Ta dalilin Kallo, ko shafa, da Tunanin Jima’i.

2. BAMBANCI YAYIN FITARSU:

Shi Maniyyi yana fita ne yayin da sha’awa ta kai Kololuwa, kuma akan samun mutuwar Jiki, har tsattsafowar gumi bayan fitarsa.

Shi kuma Maziyyi yana fita ne yayin motsawar sha’awa kadai. Kuma ba’a samun mutuwar jiki bayan fitarsa.

3. BAMBANCI A HUKUNCINSU:

Fitar Maniyyi tana wajabta wanka, ita kuma fitar Maziyyi bata wajabta wanka. Sai dai Mutum zai je ya wanke al’aurarsa baki daya.

Malamai sunyi sabani akan Shin Maniyyi Najasa ne, ko ba najasa bane. Amma shi Maziyyi kowa ya yarda cewa shi NAJASA ne.

MAGANAR QARSHE:

Maniyyin Maza: Fari ne yana da kauri da yauki.

MANIYYIN MATA: Fatsi ne, bashi da kauri, kuma yana da yauki yauki.

Ana yin wanka saboda fitarsa. Kuma Malaman Malikiyyah sunce Shi maniyyi Najasa ne.

MAZIYYI : Na maza da Mata duk iri daya ne. Kuma fari ne tsinkakke. Garai garai yake kamar ruwan sha.

Yana karya alwala, kuma ana wanke al’aura baki dayanta sabosa fitarsa. Kuma za’a wanke tufafin da ya taba.

WADIYYI : Yana fita ne akarshen fitsari. hukuncinsu daya da fitsarin. Za’a wankeshi ne kawai.

WALLAHU A’ALAM.

The post BANBANCIN MANIYI DA MAZIYYI NA MATA DA NA MAZA appeared first on MUJALLARMU.

MAGANIN FITSARIN KWANCE A SAUWAKE BABBA KO YARO

$
0
0

Ita wannan matsalar ana iya shawo kanta ne ta hanyoyi guda biyu kamar haka :

MAGANI : A nemi kwayoyin habbatus sauda, a rika yiwa yaro hayaki dasu. Kuma yana dan tsugunawa akan hayakin. Sannan kuma a rika gauraya masa habbatus sauda din yana shan cokali guda tare da zuma. Ko kuma ya shafe jikinsa da man Habbatus sauda din wanda akayi tofi acikinsa. In sha Allahu zai dena.

2. ADDU’A : Arika tofa masa wannan addu’ar, ko kuma akoya masa ya rika yinta da kansa, ko kuma a rubuta masa ajikin takarda ya sanya ajikinsa yayin da zai kwanta.

Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bn Amru bn Al-As Sahabin Manzon Allah (saww) yana rataya ma ‘ya’yansa Qanana wannan addu’ar. Gata nan kamar haka :

“أعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وعقابه ومن شر عباده و من همزات الشياطين و أن يحضرون”.

‘A’udhu bi kalimatil Laahit tammati min ghadhabihee wa ‘iqabihee wa min sharri ibadihee wa min hamazatish shayateen wa an yahdhurooni.

FASSARA : Ina neman tsari da cikakkun kalmomin nan na Allah daga fushinsa da Uqubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin fizge-fizgen shaitanu, kuma (ina neman tsarinsa) kada su halartoni.

In sha Allahu koda babban mutum ne yake fama da matsalar fitsarin kwance, in dai ya lazimci wadannan abubuwan tare da gaskatawa zai ga biyan bukatarsa.

WALLAHU A’ALAM.

The post MAGANIN FITSARIN KWANCE A SAUWAKE BABBA KO YARO appeared first on MUJALLARMU.

turkashi wata sabuwa BINCIKE YA FADA GIDAN SARAUTAN KANO, BA DAGA KAFA INJI BUHARI

$
0
0

Dama tun kwanaki NAIJ.com ta kawo maku rahoto cewa Jama’a sun fara ganin cewa kalaman Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na nema yayi yawa ya wuce gona da iri. Har aka fara kishin-kishin din cewa ana kokarin sauke sa daga kujerar sa. Wani Marubuci kuma Dan Jarida mai suna Ja’afar Ja’afar yayi wani rubutu inda ya bayyana irin kudin da fadar Kano ta rika batarwa wajen sayen manyan motoci da kuma hawa shafin yanar gizo.

Hukumar yaki da zamba da kuma karbar korafi ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta fara bincikar Masarautar Jihar domin jin yadda aka kashe makudan biliyoyi cikin kankanin lokaci. Wani daga cikin manyan masarautar dai yace za su yi bayani ba da jimawa ba. Kwamitin da aka nada tayi bincike game da su Babachir David Lawal ta soma aiki. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanawa Osinbajo cewa duk wanda aka samu da laifi a dakatar da shi ba tare da wata-wata tun kafin a kammala binciken.

 

The post turkashi wata sabuwa BINCIKE YA FADA GIDAN SARAUTAN KANO, BA DAGA KAFA INJI BUHARI appeared first on MUJALLARMU.

ABUN DARIYA ABUN HAUSHI ku karanta girma ya fadi

$
0
0

Manyan ofishosin hukumar sojin kasa guda 2 sun tsere daga harin Boko Haram bayan sun gano bama-bamai da mayakan Boko Haram sun binne a karkashin kasa

Mukaddashin mai magana da yawun hukumar sojojin Najeriya mai suna Sani Usman ne ya bayyana hakan acikin wata takarda a garin Maiduguri, wani birnin jihar Borno.

Manjo Muhammad Alkali, wani babban kwadinata na shalkwatar hukumar sojin Najeriya da kuma mukaddashin Janara Ofisha Kwamanda na hukumar sojin kasa ta dibishan 7 mai suna Victor Ezugwu ne janaral sojin kasa biyu da yan Boko Haram suka so kashe.

Sun fuskanta bama-bamai wadanda an binne a jamsin Banki da titin Pulka, tsawon kilomitar 6 zuwa garin Firgi a jihar Borno. “Manyan ofishoshi biyu sun kai ziyara ga dakarun 26 Task Force Brigade da suka yi aikin Operation Lafiya Dole da kuma yakin Operation Deep Punch.” Inji Birigadiya janar Usman

The post ABUN DARIYA ABUN HAUSHI ku karanta girma ya fadi appeared first on MUJALLARMU.


TATTAUNAWAR MU DA WASU ‘YANMATA kan yanda suke jawo hankalin maza

$
0
0

A shirin mu na mata, yau dandali ya zanta da wasu samari da ‘yan mata inda suka yi mana bayani akan yadda suke bayyana ra’ayin su musamman idan suka ga wadanda suke so. Mun fara tattaunawar ne da ‘yan mata inda budurwa ta farko ta ce;

“A gaskiya idan na ga saurayin da nake kauna, ko ban fada mashi ba, ni zan san yadda zan jawo shi a jika har ya gane cewar lallai ina son shi. Idan kuma mai mata ne, zan rika jan dansa a jiki ina bashi kyaututtuka da sauran abubuwa makamantan su, idan bashi da mata kuma, kanen shi zan fara neman jawo wa a jiki, idan kuma akwai shakuwa tsakanin mu to zan iya fada mai.”

Mai magana ta biyu kuma cewa ta yi, kawai abinda take yi shine yawaita dariya da murmushi da zarar sun yi ido hudu da juna. Ta kara da cewar koda magana ya ke da wasu, zata rika yawan shiga maganar sa, ta ce uwa uba ma idan ta gamu da shi a hanya har wani taku take canzawa.

Wata kuma cewa ta yi yawaita kwalliya da zata ja hankalin saurayi ba wata abu mai wuya ba ce, ta kara da cewa ita a nata ra’ayin bazata iya bude baki har ta fada ma saurayin tana son shi ba domin akwai kunya.

Da muka waiwayi samari kuma, wani matashi ya bayyana mana cewar lallai lamarin yakan sa ya fara ba budurwar kyauta da haka har zai jawo hankalin ta.

The post TATTAUNAWAR MU DA WASU ‘YANMATA kan yanda suke jawo hankalin maza appeared first on MUJALLARMU.

MECECE ILLAR AURAN MATAR DA TA GIRMI MUJIN TA

$
0
0

Matasan Arewa na da wata al’ada ta tsangamar matashin da ya auri matar da ta fi shi shekaru, ba don komai ba sai don suna ganin ba zai samu yadda yake so a matsayinsa na maigida wanda akalar auren ke hannunsa ba.

Al’adar ba ta tsaya kan Hausawa ba kawai ta game har sauran kabilun da ke yankin Arewa, wadanda suke ganin al’adar ’yan Arewa ce ya zama miji ya girmi matarsa, wanda a ganina don mutum ya auri wacce ta girme shi ba wani aibu ba ne, idan da soyayya da kauna da aminci a tsakaninsu. Shi ya sa a kudanci ba wani abu ba ne don mutum ya auri wacce ta fi shi shekaru.
A wadansu wuraren ma har suna ake sanya wa mutumin da yake soyayya ko kuma ya auri wacce ta girme shi. Sai ka ji ana kiransa mijin tsohuwa ko a rika ce masa ya auri babarsa. Tun ba ma a ce bazawara ce wacce take da shekaru da yawa ba, kuma ta dauki shekaru da dama rabon ta da aure, ai sai ka ji ana ta yin maganganu da yawa a kan ta.
A ganina abin da ake bukata a aure shi ne tsayayya da kauna. Idan har matar da za ka aura tana sonka to babu shakka ka samu abin da ake bukata. Yawa ko karancin shekarunta ko ba shi da wani muhimmanci mai yawa.
Hasali ma abin da samarin yanzu ba su gane ba shi ne bazawara mai yawan shekaru wacce ta goge da rayuwa ta fi budurwa mai karancin shekaru dadin zama. Kuma ta fi ta sanin soyayya da yadda ake yin ta, sannan kuma ta fi ta iya abubuwa da dama na zamantakewar aure saboda ta yi aure ta ga yadda yake.
Dadin dadawa, idan ma matar ba ta taba aure ba mudddin tana da yawan shekaru za ka ga ta fi wacce ba ta da yawan shekaru fahimtar rayuwa. Domin yawan shekarunta zai sanya ta ga abubuwa da yawa na rayuwa wacce wadda take da karancin shekaru ba ta gani ba.
Mata masu karancin shekaru na wannan zamani sun rasa abubuwa da yawa. In dai ba ka yi sa’a ba da ka auri yarinya mai karancin shekaru in ba ka kai zuciya nesa ba kafin wata guda sai ka sake ta, saboda irin katobarar da za ta rika yi maka da kuma yarintar da za ta rika nuna maka musamman wajen dafa abinci da kwanciyar aure da sanin abin da kake bukata. Sai dai idan ka yi sa’ar gaske kamar yadda na yi, to shi ne za ka samu mace mai karancin shekarun da za ta rika yi maka abin da kake so ba tare da wata matsala ba.
Wani abokina ya taba shiga cikin tsaka-mai-wuya lokacin da ya yi yunkurin auren wata budurwa wacce ta dade ba ta samu miji ba, kuma ga shi ta fi shi yawan shekaru. Har sai da ta kai ’yan uwansa da mahaifiyarsa suka nuna bacin ransu a gare shi. Haka ma ya taba faruwa da wani wanda ya ya yi yunkurin auren wata bazarawa da ta fi shi yawan shekaru.
Wani matashi ya taba auren wata tsohuwa da ta yi jika da shi a Arewacin Najeriya. Mutane suka rika gutsuri-tsoma dangane da aure. A ganina bai yi kuskure ba domin a wajen ta ya ga soyayyar da yake nema shi ma da kansa ya fada cewa ta fi nuna masa soyayya a kan ’yan matan da yake nema.
Shi aure ba wani abu ba ne illa so da kauna da amince da kuma zaman lafiya. Saboda haka idan mutum ya samu macen da take da abubuwa da ake bukata komai yawan shekarun ta ni ban ga wata illa ba.

The post MECECE ILLAR AURAN MATAR DA TA GIRMI MUJIN TA appeared first on MUJALLARMU.

AMFANIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR KA/ KO KE

$
0
0

Ya na dauke da sinadarin ‘dimeric flavonoid’

A na noman wannan dan itace ne a kasashen Najeriya, da Kamaru, da Ghana, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Benin, da Kwadebuwa, da Gabon, da Saliyo, da Laberiya, da kuma Sanegal. Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin namijin goro ga lafiya.

A tarihance, likitoci a Afirka sun yi imani cewa, namijin goro na da sinadarin yakar kaska, da yashe ciki, da kuma yakar kananan kwayoyin cuta. Da farko dai likitoci na amfani da shi don maganin tari da cututtukan makogwaro, da bututun iska, da ciwon kai ko sanyin kirji, da kuma ciwon ciki. Bugu da kari, tsarin maganin gargajiya na Afirka ya nuna masu matsalar hanta ka iya tauna namijin goro.

Wannan dan itace na taimaka wa wajen maganin dukkan nau’i na tari, a na kuma amfani da shi wajen maganin sanyi.Yawanci kuma ya fi amfani wajen kakkabe mashako, da tari, da toshewar hanci, da kuma majina. Namijin goro ya na taimakawa wajen yakar miyagun cututtuka kamar Ebola, ya na kuam dauke da sinadaran yakar dadewar fata da sauransu. Ya na kara karfin kwaranyar jini ga mutanen da ke da matsala da bututun da ke dauko jini daga zuciya. Sannan ya na taimaka wa garkuwar jiki,domin binciken kimayya na musamman ya tabbatar da cewa, yawan amfani da shi na ba da kariya ga garkuwar jikin dan adam. Har ila yau Namijin goro na warkar da ciwon gwiwa wajen rage mata radadi sosai yana kuma amfani wajen jin yunwa sannan ya na sa jin kishirwa.

 

The post AMFANIN NAMIJIN GORO GA LAFIYAR KA/ KO KE appeared first on MUJALLARMU.

MAGANIN KARFIN MAZA A SAUWAKE

$
0
0

Ka samu Mazakutar Bijimin Sa. Wanda ba’a dandake shi ba. Ka dafa tare da ‘danyar chitta da Manguli. (Kar a sanya Gishiri ko maggi, amma za’a sanya dukkan kayan Qamshi). Idan ya dahu sai ka rika ci.

Zaka rika maimaitawa daga lokaci zuwa lokaci.

Idan kuma Qarfi ake bukata, asamu Mazakutar Karakanda (wani dabba mai Qaho reshe-reshe). Idan ba’a samu na Karkandan ba, anemi na namijin Gada (akuyar jeji).
Idan shima bai samu ba, sai ayi dana ‘Dan-Akuya wanda ba’a dandake ba.

Ka daka Mazakutar aturmi.
Sannan ka shanya ya bushe. Idan ya bushe a rika ci da cukwi.

To insha Allahu Mazakutarka zata girma kuma zaka samu Qarfi.

Wallahu a’alam.

The post MAGANIN KARFIN MAZA A SAUWAKE appeared first on MUJALLARMU.

TARON BITA NA YINI DAYA A JAHAR ZAMFARA

$
0
0

Gagarumin Taron wayar da kan matasa da wasu masu kishin jahar Zamfara. Sunka shirya, domin yin wani shiri irinsa na farko, Akan hanyoyin KASUWANCI TA HANYAR YANAR GIZO!

ZA A YI WADANNAN TARON KAMAR HAKA;

RANA; Assabar 29-4-2017

LOKACI: 8:00 NA SAFE.

WURI: SAKATERIYAR JB BALA YAKUBU.

A yayin yin wannan workshop din na yini. Daya. Za a wayar da kan matasa Akan hanyoyin da za su nemi na Kansu ta hanyar KASUWANCI a kafofin sada zumunci.

Haka za a koyar da mutane yadda ake; gyaran hotona, da biyoyi dss.

Haka za koyawa matasa wasu muhimman ababe da sunka shafi kwamfuta. Da hanyoyin tu’ammali da kwamfutar cikin sauki. Da dai sauran Abubuwa matara kama da haka.

Kai dai ka KASANCE da mu a lokacin da za a yi wannan Gagarumin taron bita.

Note: kyauta ne, za a yi wannan bitar. Amma in kare Mai so zai karbi takardar shedar halartar wannan taron bitar (Certificate of attendance) Akan naira Dari biyu da hamsin (250) kacal! Amma fa ga Mai so kurrum.

Domin Karin bayani zaka iya tuntunbarmu

A wadannan numbers

Kamal Dansadau: 08034208823

Activist Muhammad Lawal Gusau: 08065983688

Nasiru Umar: 07059592007

Rufai UB Gusau: 08106580400

Ko ni Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496

Allah ya sa mu karu da Abunda za mu koya.

Zaka iya rajista a wannan form din.

 

The post TARON BITA NA YINI DAYA A JAHAR ZAMFARA appeared first on MUJALLARMU.

KUDIRIN MINISTAR KUDI GA TALAKAWAR NAGERIYA

$
0
0

Ministar kudi ta kasa NAJERIYA watau Kemi Adeosun ta bayyana cewa yanzu abin da ke gaban ta shi ne talakan Najeriya ya samu ya amfana. Ministar tace yanzu ta talakawan Najeriya ta ke.

Ministar ta dauki kusan shekara guda tana shiryawa inda har aka zana mafita daga kangin tattalin arzikin da Najeriya ta burma ciki. Ministar ta bayyana wannan ne a wata ganawa da tayi da Jami’an bankin Duniya da IMF mai bada lamuni.

Daga cikin matsalolin da ake fama da su a Najeriya akwai rashin isassun gidajen zama don haka ne wannan Gwamnati ke shirin gina gidaje. Ministar tace za kuma ayi kokari wajen ganin an wadata Najeriya da abinci da tsaro da ma lantarki. Akwai kishin-kishin din Shugaba Buhari na neman sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma daga cikin wadanda ake tunani zai maye gurbin akwai Hameed Ali na Hukumar kwastam wanda ya saba aiki da shugaba Buhari tun ba yau ba.

The post KUDIRIN MINISTAR KUDI GA TALAKAWAR NAGERIYA appeared first on MUJALLARMU.

ina neman shawaran ku AKAN ME GIDANA DAN WATA MANUFAR SA

$
0
0

Salam, Sunana Halima Kabir daga garin KADUNA, ni matar Aure ce kuma dai dai bakin gwargwado ina ma mijina biyayya kuma nima yana min duk abinda nake so yana sona nima ina son shi, kuma wani abu bai taba shiga tsakanin mu ba sai dai zaman lafiya. domin baya son bacin raina nima bana yarda ran shi ya baci.

A takaice dai muna matukar jin dadin zaman auren mu har mutane ma suna sha’awan yadda muke da mijina.

Kawai satin da ya wuce sai ya zo min da wata sabuwar dabi’a wacce a tunani na ta kauce ma addini, wannan dabi’a itace wai yana so in rika saka AZZAKARIN shi a bakina ina sha wai hakan zai sa shi yaji dadi kuma ya kara sona.

Toh a gaskiya banyi ba, na fito fili na fada masa ba zan iya ba, yanzu haka mijina yayi matukar fushi dani ko abincina baya ci kuma sai dare ya raba yake dawowa gida wani lokaci ma baya kwana a gida idan nayi masa magana sai yace wai aiki ne yayi masa yawa.

Tun lokacin baya dariya dani har yau.

Yan uwa ina matukar bukatar Addu’ar ku kuma ina neman shawara domin na kasa sukuni ko bacci bana iya wa dalili kuwa shi ne ina tunanin kamar ALLAH yana fushi dani domin naki bin umarnin mijina.

1. TAMBAYA TA ana itace shin ALLAH yana fushi dani?

2. Idan na sha azzakarin sa babu laifi?

The post ina neman shawaran ku AKAN ME GIDANA DAN WATA MANUFAR SA appeared first on MUJALLARMU.


LABARIN WATA MATAR AURE A FACEBOOK DA WANI SAURAYI

$
0
0

Wata matar aure ce a Abuja takeyin 2go se ta hadu da wani saurayi suka ringa chatting har ma suka kasance masoyan juna amma bata taba gaya masa ita matar aure ce ba.

Saurayin nan kuma sonta ya kamashi sosai, matar kuwa mijinta me kudi ne sosai kuma babban dan kasuwa ne international Business yakeyi wani lokaci idan yaje qasar waje har watanni yakeyi bai dawo ba.

Watarana saurayin nan yayi sati daya be shigo online ba, sai ta kira wayarsa ta tambayeshi meyasa baya zuwa online sai yace; baida Kudi, sai tace; ya turo mata Account Number dinsa.

Matar nan kuwa taje Bank ta turo masa dubu hamsin (50,000) mutuminka yayi murna sosai amma ya tambayeta ina ta samo kudin tace; “kudina ne da iyayena kebani wadanda nake tarawa shine na baka”

Saurayin nan yagano tana sonshi sosai sai yace yana so su hadu sai suka shirya inda zasu hadu a Minna Niger State a UK Bello.

Sai matar ta hawo mota tazo gurin bayan awa daya shima yazo sai suka hadu yaganta tanada kyau sosai amma zuciyarsa na gaya masa wannan kamar matar aure ce fa idan ma ba matar aure ce ba to bazawara ce amma bai tambayeta ba.

Sai matar tace suje Mr. Biggs suci abinci da suka zo aka kawo musu abinci matar ta fita ta dauko drinks a cikin mota sai ta zuba maganin bacci a cikin drinks din data kawo masa yasha bayan sun gama sai suka shiga mota kawai ya fara bacci har matar ta kaishi Abuja cikin wani gida da take ginawa.

Daya farka sai ya fara Kalmar shahada yana tambayarta a ina yake sai tace; na kawoka Abuja wannan kuma gida dakake ciki nawa ne ina buqatar kayi amfani dani kuma ni matar aure ce zanyi maka duk abinda kake so, tayi-tayi dashi yaqi sai matar tace to ya jirata bari ta kawo masa abinci ta hau mota taje cikin gari sai tayi accident da wani Learner kuma abokin mijinta ne.

Matar taji ciwo/rauni sosai mutum baiji ciwo ba ya dauke ta ya kaita asibiti, kuma saurayin nan dayake cikin gidanta bacci ya kwasheshi, to dama masu aiki na zuwa suyi mata aiki a gidan da sukazo suka ganshi sai suka kira yan SANDA suka kamashi.

Bayan yan SANDA sun kamashi suka tambayeshi “me yakeyi a cikin gidan kuma waya kawo shi?” Saurayin Yace: “na fito daga Sokoto ne, na rasa gurin kwanciya kuma banda kudin da zan kwana a Hotel”.

Yan SANDA sukayi bincike dakyau suka gano cewa bashida laifi kuma ba komai yazo sata ba, amma sukace sai mai gidan tazo ta ganshi kafin su sakeshi.

Sun nemi matar da keda gidan sukaji labarin tayi accident suka tsare shi har ta warke.

Bayan tawarke aka gaya mata abinda ya faru tace a kawoshi aka kawo matashi ta fara roqonsa gafara tana cewa nagodewa ALLAH dana hadu dakai, kuma naji dadin irin yanda ka kare mutuncinka naji dadi sosai.

Tunda nagano kai mutumin kwarai ne mai zai hana ka auri ‘yata wacce take El~Amin International Secondary tana J.S.S 3 ne nasan zaka iya jira tagama Secondary se kuyi aure.

Saurayin nan ya amince kuma matar ta bashi kudi dayawa kuma ta masa alqawarin aiki a kamfanin mijinta.

To jama’a kunga yanda riqon amana yake da garabasar lada

The post LABARIN WATA MATAR AURE A FACEBOOK DA WANI SAURAYI appeared first on MUJALLARMU.

MASU GUDU SU GUDU, ZA A MAKA WANI TSOHON GWAMNA A KOTU

$
0
0

a yau Talata ne ake shirin gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Neja watau Muazu Babangida Aliyu a Garin Minna babban Birnin Jihar na Neja a babban Kotun tarayya. Ana dai zargin Muazu Babangida Aliyu da wasu tarin laifuffuka a lokacin da ya rike kujerar Gwamnan Jihar na shekaru 8 daga 2007 har zuwa 2015. Tun kwanaki dama dai Hukumar EFCC ta damke sa bayan an bayyana cewa bai amsa gayyata ba.

Labarin da mu ke ji dai shi ne Jama’an gari na shirin tarbar tsohon Gwamnan na su da jifa yayin da aka shirya shigar da shi kotu. Dalilin haka ne aka tanadi Jami’an tsaro domin hana kawo wani rikici.

The post MASU GUDU SU GUDU, ZA A MAKA WANI TSOHON GWAMNA A KOTU appeared first on MUJALLARMU.

fata me kyau GWAMNATI ZATA SAMAR DA AYYUKA 900,000

$
0
0

Gwamnatin Jihar Legas na shirin samar da ayyuka ga kusan Miliyoyin Jama’a. LSETF ta bayyana shirin samawa Jama’a har 900,000 sana’a a fadin Jihar daga yanzu zuwa shekarar 2019. Shugaban LSETF Akintunde Ambode ya bayyana hakan kwanan nan kamar yadda

NAIJ.com ta samu labari. Hakanan kuma za a koyawa Jama’a da dama sana’a tare da ba da hoto na ayyuka lokaci bayan lokaci.

Gwamnatin dai ta hada kai da Hukumar NEPC mai bada kwarin gwiwa wajen harkar fita da kaya wajen kasar da kuma sauran Hukomi irin sy NAFDAC da Kwastam ta kasa. Ana dai fama da rashin aikin yi a kasar nan.

The post fata me kyau GWAMNATI ZATA SAMAR DA AYYUKA 900,000 appeared first on MUJALLARMU.

RUWA SUN ZAMA TAMKAR ZINARI A GARIN GUSAU.

$
0
0

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
25-4-2017
Duk cewa, Ruwa su ne sinadari na farko da duk wata halitta take so domin rayuwa. An wayi gari talakawan jahar Zamfara, muna matukar shan wahala wajen samun ruwan tare da shan Ruwa marar tsafta, Musamman a garin Gusau da ke zama shalkwatar jahar Zamfara.
Domin yanzu haka, Akan samu Ruwa, na kasa da awanni biyu ne kacal! A kullum. Haka zalika mafiya yawan fanfonan da kan kawo Ruwan sun dena kawo ruwan, Saboda karancin ruwan. Dan haka yanzu mutane kan girgine magudanun Ruwa ne, cikin kwatoci Suna samun ruwan, Duk da Alhamdulillahi sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakkiya, ya yunkuro domin taimakawa wajen gyara wadannan wurare ta yadda za a samu Ruwa masu Tsabta. Amma sai dai kash! Yanzu kusan in ce ruwan sun koma in Yau sun zo to gobe ba su zuwa.
Wanda yanzu haka shekaranjiya ba a kawo ruwan ba Yau ma haka. Duk da cewa gwamnatin jahar Zamfara ta ware maguddan kudade domin gyaran wannan matsala sai dai har yanzu ba mu gani a kasa ba. Dan haka muna Kira ga ita gwamnatin Dan Allah ta kara sanya ido a wannan matsalar. Domin irin yadda ake samo Ruwa yanzu na daya daga cikin ababen da kan kawo, barkewar zabo da amai, malaria da sauran cutukka matara kama da haka.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
25-4-2017

The post RUWA SUN ZAMA TAMKAR ZINARI A GARIN GUSAU. appeared first on MUJALLARMU.

MAGANIN SANYIN KASHI

$
0
0

1. Man Jirjeer.
2. Man tafarnuwa.
3. Man Habbatus Sauda.
4. Man kanumfari.
5. Man kustul Hindi. (not compulsory).

Ka hadasu waje guda, ka gauraya ka karanta ayatush shifa’i aciki, sannan ka raba gida biyu. Ka rika shan rabi, kuma kana shafa rabi adukkan sannan jikinka. musamman Qafafunka da hannayenka.

Shi wanda zaka sha din, zaka iya zuba cokali guda acikin zuma sannan kasha. In sha Allahu zaka samu lafiya da izinin Allah.

Amma fa duk wadannan mayukan ka nemi Original na kampanin Hemani ko na Misra.

WALLAHU A’ALAM.

The post MAGANIN SANYIN KASHI appeared first on MUJALLARMU.

Viewing all 3050 articles
Browse latest View live