Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

JAMI’AN TSARO SUN FARA ZAKULO MASU HANNU DUMU DUMU A RIKICIN KABILANCI A ILE IFE

$
0
0

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti mai zaman kanta wanda ke bincike kan hakikanin abin daya faru

Wani bincike ya nuna cewa yanzu haka mutane guda biyar da ake zargi da kitsa rikicin Ile Ife wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30 na hannun jami’an tsaro.

Mutanen dai su ne:

2. Jimoh

3. Mista Abiodun

5. Damola.

Tuni dai gwamnatin kasar, ta ce za ta hukunta duk mutumin da aka samu da hannu a rikicin.

Ministan harkokin cikin gida, Abdurrahman Danbazau ne ya nanata hakan, yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai Ile Ife ranar Alhamis, 16 ga watan Maris a yammacin kasar.

Da man dai gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti wanda yake bincike kan hakikanin abin da ya faru.

Abdurrahman Danbazau ya ce ba za a kyale duk wanda aka samu na da hannu a rikicin ba.

The post JAMI’AN TSARO SUN FARA ZAKULO MASU HANNU DUMU DUMU A RIKICIN KABILANCI A ILE IFE appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>