Cibiyar fataucin mayagun kwayoyi da kula da tsaftar abinci da ruwan sha wato NAFDAC wata gobara a yau ta lashe rumbun ajiyar kayayyakin kyamikal
Wannan Rahoto yana zuwa muna ne daga JARIDAR PUNCH
inda take cewa ita dai wannan gobara babu wanda yasan sanadiyyar tashin ta,sai dai kuma ana kyautata zato gobarar ta fara tashi ne daga ofis din ma’aikatan dake aiki inda daga bisani wutar ta garzaya har zuwa wajen ajiyar kayyaykin kyamikal kamar irin su Ethanol
Rahoto ya kara cigaba da cewa wannan gobara ta tashi ne a misalin karfe 3pm na rana inda kuma ba’a samu nasarar kwantar da ita ba sai misalin 6pm a lokacin da ma’aikata yan kwana kwana suka iso domin kashe wutar
Wani babban manaja na jihar legas dake jagorantar hukumar ta NAFDAC Mr Adesina Tiamiyu yace anyi kokarin tsaida wutar domin gudun kada ta kai ga babban ofishin ajiyar manyan mahimman abubuwa.
Yanxu haka dai ana zurfafa bincike domin gano dalilin tashin gobarar.
The post YANZU YANZU GOBARA TA TASHI A OFISHIN NAFDAC DAKE JIHAR LEGAS appeared first on MUJALLARMU.