Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KO KUN SAN KUNGIYAR DATA CI WASANNI HAR SAU 600 A GASAR FIREMIYAR INGILA ?

$
0
0

Manchester United ta samu nasarar cin wasanni 600 a gasar Premier, bayan da ta doke Middlesbrough 3-1 a wasan mako na 29.
Hakan ya sa United ta zama kungiyar farko da ta kai wannan matakin na cin wasannin Premier a tarihi.
Wadanda suka ci wa United kwallayen sun hada da Marouane Fellaini da Jesse Lingard da kuma Luis Antonio Valencia, inda Boro ta zura kwallonta tilo ta hannun Rudy Gestede.
United din ta daga sama zuwa mataki na biyar a kan teburin Premier, bayan da ta yi kwanaki 184 a mataki na shida a gasar bana.
Haka kuma kungiyar da Jose Mourinho ke jagoranta ta buga wasanni 18 a jere a gasar ta Premier ba tare da an doke ta ba, tun rashin nasarar da ta yi a hannun Chelsea 4-0 a watan Oktoba.
Manchester United za ta karbi bakuncin West Brom a wasan da za ta buga na gaba a ranar 1 ga watan Afirilu a Old Trafford.

The post KO KUN SAN KUNGIYAR DATA CI WASANNI HAR SAU 600 A GASAR FIREMIYAR INGILA ? appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>