Kayi murabus kawai, dan majalisa ya baiwa Buhari shawara
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Wani mamban majalisan wakilai , Abdulmumini Jibrin, yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus kawai saboda lafiyarsa.

Abdulmumini Jibrin wanda mamban jami’yyar APC ne yace rashin lafiyan Buhari na shafan gudanar da aikinsa da Shugabantan kasa.
“PMB ya nemi yadda zai bar aiki.
Wannan kasa ba zata yadda da Shugaban kasan jefi-jefi ba a wannan lokacin.
” Mr. Abdulmumini Jibrin har yanzu an dakatad da shi a majalisan wakilai bayan ya tuhumci kakakin majalisan, Yakubu Dogara, akan almundahanan kasafin kudin kasa.
Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Birtaniya inda yayi kwanaki 50 yana jinya.
The post DAN MAJALISAR WAKILAI ABDULRAHMAN JIBRIN YA SHAWARCI SHUGABA BUHARI DA YAYI MURABUS appeared first on MUJALLARMU.