Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kori Wani Sojanta Da Ya Yi Wa Budurwarsa Yankan Rago
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Rundunar sojin Nijeriya ta kori wani sojan ta mai suna Sunday Umar tare da mika shi ga ‘yan sanda a bisa zargin yi wa budurwarsa yankan rago.
Tuni dai ‘yan sanda suka gurfanar da shi a gaban kuliya.
Umaru dai magidanci ne mai mata da ‘ya’ya.
Yayin da yake karin haske game da yadda lamarin ya faru, wanda ya shigar da kara a madadin ma’aikatar shari’a ta jahar Plateau T.W Awe ya bayyana cewa Umaru ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Janairu a Barikin Ladi.
Umaru ya amsa cewa Budurwar ta sa ta mutu ne bayan da suka samu sabani da shi a sakamakon kiranta da wani namiji ya yi a wayar ta.
Ya ce a lokacin, budurwar ta sa mai suna Charity Thomas ta na dakin dafa abinci sai wayar ta ta buga, da ya dauka sai ya ji muryar namiji, a don haka ya bukaci ya ji ko wanene. Ya ce maimakon a fada masa, sai aka fara zuba masa zagi.
Wannan ya sa ya tinkare ta da batun, inda ita ma ta ki fada masa ko wane, sai ma tuna masa da ta yi cewa ya na da aure.
Ya ce wannan al’amari ya fusata shi inda har ya mari Charity, ita kuma ta ce ta fasa soyayyar tunda dama iyayenta sun sha ja mata kunne akan sa.
A cewar sa, Charity ita ta dauki wuka ta caka wa kanta da abun ya ki ci ya ki cinyewa. Shi kuma sai ya zaro wukar ya yi mata yankan rago domin ya karasa ta kawai.
Daga bisani kuma ya jefar da gawar ta a waje.
Da safiya ta yi sai ya tafi wajen aikin sa inda ya nemi izinin zuwa ganin iyalinsa.
Awe ya ce mazauna unguwan ne suka tsinci gawar Charity sannan suka sanar da hukuma kafin nan a ka kama Umaru.
Ya ce an samu hotunan gawar Charity a wayar sa, wanda ya dauka bayan ya kashe ta.
Lauyan da ke kare wanda ake kara, David Adudu ya roki alfarmar kotun da ta bada belin sa, da alkawarin cewar ba zai gudu ba.
Alkali kotun Samson Gang ya bayarda belin Umaru akan kudi naira 200,000, da kuma bukatar ya kawo wadanda za su tsaya masa guda biyu.
Alkalin ya daga shari’a zuwa 25 ga watan Mayu.
The post RUNDUNAR SOJOJIN NIJERIYA TA SALLAMI WANI SOJANTA DA YAYI WA BUDURWAR SA YANKAN RAGO appeared first on MUJALLARMU.