Buhari ya yanke hukuncin karshe a kan Ibrahim Magu
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Majalisar dattawa ta bukaci shugaban kasa Buhari da ya canza Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC – Ana yunkurin wanzar da zaman lafiya tsakanin majalisar dokoki da majalisar zartarwa
Wata majiya ta nace kan cewa shugaban kasa ba zai sadaukar da Magu ba A yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi yunkurin sasantawa da majalisar dattawa, akwai rahotannin cewa ya yanke hukuncin karshe a kan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC.

Mujallarmu.com ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta dakatar da tantance kwamishinonin hukumar zabe 27 sakamakon ci gaba da gabatar da Magu a matsayin shugabna hukumar EFCC duk da shawarar da majalisar ta ba shugaban kasa na cewa a cire sa sannan a maye gurbin sa da wani. Buhari ya yanke hukuncin karshe a kan Magu yayinda ya yi zaman lafiya da majalisa Buhari na kan bakar sa a kan Magu Har ila yau dangantakar dake tsakanin majalisar dokoki da majalisar zartarwa ta samu tangarda sakamakon kin gurfanar wasu jami’ai a gaban majalisar dattawa duk da sammaci da aka aika masu.
A ranar Laraba, shugaban kasar ya shirya wata kwamiti karkashin jagorancin mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo don duba da kawo karshen al’amarin.
Duk da wannan, jaridar Punch ta ruwaito cewa wata majiya a fadar shugaban kasa tace Buhari baya da shirin cire Magu.
Majiyar ta bayyana cewa koda dai shugaban kasa na da ra’ayin zaman lafiya, yana nan tare da Magu. Majiyar ta kuma ce mambobin kwamitin sulhun sun kasance tsofaffin sanatoci wadanda zasuyi amfani da kwarewarsu gurin kawo karshen al’amarin. Bidiyon wani mutumi da yayi danasanin kasancewar sa mamba a jam’iyyar APC.
The post SHUGABA BUHARI YA YANKE HUKUNCIN KARSHE AKAN IBRAHIM MAGU BAYAN ZAMAN SULHU DA YAYI DA YAN MAJALISA appeared first on MUJALLARMU.