Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

MAFI YAWANCIN ALMAJIRAN KANO SUN FITO DAGA JAMHURIYAR NIJAR DA CHADI-GANDUJE

$
0
0

 Yawancin almajiran Kano sun fito ne daga Chadi da Nijar – Ganduje

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Kwanan nan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi hira yan jarida kan al’amuran kasa daban-daban ciki harda mastalar yawan almajirai a jihar Kano.
       
Yawancin almajiran Kano sun fito ne daga Chadi da Nijar – Ganduje Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje Da aka tambayi gwamnan kan dalilin da yasa matsalar almajirai yaki ci yaki cinyewa a Kano duk da kokarin da akeyi don shawo kan matsalar.
Mujallarmu.com ta ruwaito inda Gwamnan yace: “Mun gudanar da bincike a kan al’amarin almajirai.
Muna da almajirai sama da miliyan uku a jihar kano. A cikin binciken mu, yawancin almajirai ba yan asalin jihar Kano bane.
Wasu sun fito ne daga jumhuriyar Nijar da kasar Chadi.
Wasu kuma sun fito ne daga sauran jihohi, musamman daga Arewa maso yamma da Arewa maso gabas.
“Mun dauki hanyoyi biyu; daya shine zamu gabatar da wani hanyar hadin kai, ta hanyar samar da wani darasi a makarantun Qur’ani da zai dauki nauyin makarantun Almajirai. “Zamu gabatar da darusa irin su Lissafi (Mathematics), harshen turanci (English) da kuma nazarin zaman jama’a (Social Studies) wanda daga nan zasu iya zana jarabawar kammala makarantar Firamare.
“Hanya ta biyu shine shawo kan sauran gwamnoni da su hana mayar da yaran makaranta Kano. “Yanzu, duk dalibin da ya zo a matsayin almajiri, muna da wadanda zasu mayar da su zuwa inda suka fito. Amma wannan ba shine maganin matsalar na din-din-din ba. Maganin matsalar shine jihar ta sanya dokar da zai hana wadannan yaran yin kaura.

The post MAFI YAWANCIN ALMAJIRAN KANO SUN FITO DAGA JAMHURIYAR NIJAR DA CHADI-GANDUJE appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>