Hukumar EFCC ta gano N400 million a wata kufaina a jihar Legas (Hotuna)
Marubuci;Haruna Sp Dansadau
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gano kudi akalla N400 million a wata shago na kasuwan canj a jihar Legas

Kudinda aka gano a kufai Wannan abu na faruwa ne kimanin wata daya da gano wasu makudan kudi a babban filin jirgin saman jihar Kaduna.
Hukumar ta gano kudi N448, 850,000 a wani shago da ke LEGICO Shopping Plaza, Ahmadu Bello Way, Victoria Island, Lagos.

Kudaden na boye cikin jakukuna wanda aka fi sani da Ghana Must Go jerin N500 da N1000 inda akai jiran canza su.
Dandalin Mujallarmu.com ta tattaro cewa hukumar ta bayyana wannan abu ne a daren Juma’a misalin karfe 8 a shafin ra’ayi da sada zumuntarta cewa ta gano makudan kudi a wata kufaina.
A yanzu dai, hukumar EFCC ta fara bincike domin gano wadanda keda mamallakin kudin amma har yanzu babu wanda ya ga fito yace nashi ne.
The post LABARI CIKIN HOTUNA:HUKUMAR EFCC TA GANO MILIYAN 400 MAKARE ACIKIN JAKUKKUNA A WATA PLAZA DAKE LEGAS appeared first on MUJALLARMU.