Matan da ya haramta a aura sun kasu kashi biyu:
(1) Wadanda su ka haramta har abada – su ne:
(A) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda dangantaka ta jini da mijin: kamar yanda ya zo a Suratun Nisa’i aya ta aya ta 23, kamar haka:
(i) Uwaye – wato mahaifya da kakanni mata ta bangarorin uwa da uba, ko mai nisansu; (ii)’Ya’ya mata – wato ‘yar mutum ta cikinsa da ‘yar dansa ko ‘yarsa, kome nisansu; (iii) ‘Yar uwa – wa ya ko kanwa, uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya;(iv) Gwaggwanni – wato ya ko kanwar uba, da kuma gwaggwannin babansa, da babarsa da kakanninsa (maza da mata); (v) Innoni/Yakumbo – wato ya ko kanwar uwa, da kuma innonin mahaifinsa da mahaifiyarsa da kakanninsa (maza ko mata); (vi) ’Ya’yan ‘Yan uwa maza – wato ‘yar wansa ko kaninsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss; (vii) ’Ya’yan ‘Yan uwa mata – wato ‘yar yarsa ko kanwarsa (uwa daya uba daya, ko uba daya, ko uwa daya) da kuma ‘ya’yan ‘yayansu maza ko mata dss.
(B) Mata bakwai (7) wadanda a ka haramta saboda shayarwa: Su ne wadanda su ka haramta a sama kamar yanda Manzon Allah (SAW) ya ce: ((Shayarwa na haramta duk abin da dangantakar jini ke haramtawa)) da sharadin: (i) Yaron ya sha nonon matar (sha na koshi) a kalla sau biyar, (ii) kuma dukkanin shayarwar ta faru ne kafin yaye.
Idan wadannan sharudda sun cika, to yaron ya zama dan wannan mata, kuma ‘ya’yanta sun zama ‘yan uwansa, ko da an haife su kafin ko bayan shayar da shi. Haka kuma, dukkan ‘ya’yan mijin da take shayar da dansa lokacin shayarwar sun zama ‘yan uwansa ko da daga wata matar suke ba ita ba. Amma ya kamata a lura a nan cewa, ‘yan uwan wanda a ka shayar din banda ‘ya’yansa, ba su da wata alaka da wannan shayarwar da hukun-hukuncenta. Don haka, ya halatta ga dan uwansa na jini ya auri matar da ta shayar da shi ko ya auri ‘yan uwarsa ta shawayarwa. Sai dai kuma ‘ya’yan dan da a ka shayar sun zama ‘ya’yan matar da ta shayar da shi da kuma uban dan da ta ke shayarwa a daidai lokacin da ta shayar da shi…
(C) Mata Hudu (4) wadanda a ka haramta saboda aurataiya: Su ne kamar haka:
(i) Matan Uba – wato matan mahaifinsa da kakansa (na uwa na uba) komai nisansa. Kuma da zarar an daura aure tsakanin mutum da wata mata, to ta haramta ga ‘ya’ayansa komai nisansu, ko da bai tare da ita ba. (ii) Matan ‘Ya’ya – wato matan ‘ya’yansa komai nisansu, da sharadin dan ya tare da matar. (iii) Babar Matarsa – wato mahaifiyar matarsa da kakarta, komai nisanta. Don haka, da zarar mutum ya auri mace, to babarta da kakanninta (na uwa da na uba) sun haramta gareshi, ko da bai tare da ita ba, komai nisan kakannin. (iv) ‘Ya’yan Matarsa – da ‘ya’yan ‘ya’yansu (maza ko mata) da kuma jikanninsu komai nisansu, matukar dai ya tare da mata. Amma da saki ya afku kafin ya tare da matar, to wa]annan ‘ya’ya da ‘ya’yansu ba sa haramta gare shi, sawa’un an haife su kafin ko bayan ya aure ta.
(2) Matan da su ka haramta a aure su zuwa wani lokaci – su ne:
(A) ’Ya ko Kanwar Matarsa ko Goggonta – wato na bangaren uwa ko uba har sai lokacin da su ka rabu da ita kodai ta rasu ko kuma bayan ya sake ta kuma ta kare idda.
(B) Matar da ke cikin Idda – har sai ta kare iddar.
(C) Matarsa da ta shiga Harama – har sai ta kare aikin Hajji ko Umarar.
The post MATAN DA YA HARAMTA A AURA appeared first on MUJALLARMU.