Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

HAR YANZU ‘YAN MATAN CHIBOK SUNA RAINA SABODA HAKKIN SU YA RATAYA AKAINA-SHUGABA BUHARI

$
0
0

Har yanzu ‘yan Chibok suna raina — Buhari

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da tattaunawa da ‘yan Boko Haram don ganin an ‘yanto sauran ‘yan matan Chibok –

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu kwana guda gabanin cika shekara uku da sace ‘yan matan – Ya ja hankalin ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya kan kowa ya taimaka wajen yaki da ta’addanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da tattaunawa da ‘yan Boko Haram don ganin an ‘yanto sauran ‘yan matan Chibok da sauran mutanen da suke rike da su cikin koshin lafiya. Ya ce: “Ta hanyar masu shiga tsakani a ciki da wajen Najeriya, za mu yi dukkan mai yiwu wa don tabbatar da cewa dukkan sauran ‘yan matan sun kubuta”.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu kwana guda gabanin cika shekara uku da sace ‘yan matan fiye da 200 daga makarantar sakandaren Chibok.
Shugaba Buhari yace har yanzu ‘yan Chibok suna ran sa Har ila yau, ya ce gwamnatinsa ta dukufa wajen bai wa dakarun kasar da sauran jami’an tsaro goyon bayan da ya dace a kokarin ganin an dawo da ‘yan matan da kuma kwato yankunan da ‘yan Boko Haram suke ci gaba da iko da su. Ya ce hakan ne ya sa suka iya fatattakar ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa.
Daga nan ya ja hankalin ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya kan kowa ya taimaka wajen yaki da ta’addanci “musamman idan aka yi la’akari da yadda matsalar ta shafi kowa da kowa”. Hakazalika, ya yi kira ga ‘yan kasar da su “rika kula sosai don kai rahoton duk wani abu da ba su gane masa ba.” A sanarwar da shugaban ya fitar ranar Alhamis, ya kara da cewa, “Ya kamata mu yi farin ciki da kubutar da 24 daga cikin ‘yan matan da aka yi da kuma sauran ‘yan Najeriya da aka kwato su daga hannun ‘yan ta’addan.” Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin ganin ‘yan matan da suka kubuta sun koma cikin al’umma suna tafiyar da rayuwarsu kamar yadda suka saba. “Ina mika godiyata ga iyayen yaran nan da iyalansu, wadanda suka jure takaici da fargaba na tsawon shekara uku suna jiran dawowar ‘ya’yansu. Ina jin duk abin da ku ke ji. ‘Ya’yanku nawa ne. Don haka a wannan rana ina kiran ku da ka da mu karaya wajen fatan dawowar sauran ‘yan matan nan.,” in ji shugaba Buhari.

The post HAR YANZU ‘YAN MATAN CHIBOK SUNA RAINA SABODA HAKKIN SU YA RATAYA AKAINA-SHUGABA BUHARI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>