Wata sashen tsohuwar kasuwar dake jihar Sokoto ta kama da wuta
Jami’an hukumar kashe gobara sunyi iyakan kokarinsu wajen kawar da wutan -Har yanzu ba’a san abinda ya jawo gobaran ba Shugaban ayyuka na hukumar kashe wutan gobara na jihar Sokoto, Mustapha Mohammed yace babu wutan lantarki lokacin da gobaran ya fara.
Duk da cewan ba’a san abinda ya jawo gobaran ba har yanzu, ya lashi takobin cewa za’a gudanar da bincike sosai game da faruwan al’amarin al’amarin.
Mohammed wanda ya bayyana cewa sai da jami’ansa suka kwashe awa biyu (2) da rabi wajen kashe wutan ya
kara da cewa daya daga cikin ma’aikatan sa ya samu gocewan kashi a kafarsa na dama.
The post LABARI DA DUMIDUMIN SA GOBARA YA TASHI A KASUWAN SOKOTO appeared first on MUJALLARMU.