Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KO YA ZA’A QARE TSAKANIN SHUGABA BUHARI DA SANATOCIN NIJERIYA!!?

$
0
0

Ya za a kare tsakanin Shugaba Buhari da Sanatoci?

Marubuci:Haruna Sp Dansadau
       
Ana ta samun rikici tsakanin shugaban kasa da ‘Yan majalisar Dattawa an nada Kwamitin sulhu amma har yanzu ba a fara aiki ba.
Shugaban Majalisar yace yana bayan shugaban kasa ,Shugaba Buhari a gaban Majalisa kwanakin baya Kuna da labari cewa an nada kwamiti da zai zauna domin kawo karshen rikicin da ake ta fama tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buahri da kuma ‘Yan majalisar Dattawar kasar tun kwanakin baya.
Kwanaki aka yi ta samun takaddama tsakanin mutanen shugaban kasar da kuma Sanatocin Najeriya musamman game da shugabannin kwastam da kuma EFCC.
Har dai ta kai Gwamnatin tarayya ta ke cewa za ta nemi ta shawo kan lamarin don yana ci mata tuwo a kwarya.
Shugaba Buhari da Sanatoci a wurin liyafa Shi dai shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa babu wani rikici tsakanin su da shugaban kasa kai-tsaye inda ma ya nemi mutanen Najeriya su kara hakuri su kuma cigaba da marawa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya yace shi ma yana goyon bayan ta.
Shugaban kasa ya nada kwamiti domin sulhu da Majalisar daga ciki akwai dukkanin Ministocin kasar da su ka taba zama Sanatoci a baya irin su Minista Udoma Udoma, Minista Hadi Sirika, Minista Chris Ngige, Minista Heineken Lokpobiri da kuma Minista Aisha Jummai Alhassan dsr.
Sai dai har zuwa Ranar Talata ba su fara wani zama ba.

The post KO YA ZA’A QARE TSAKANIN SHUGABA BUHARI DA SANATOCIN NIJERIYA!!? appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>