Yaki da cin hancin Najeryia duk hira ce – Sule Lamido Yaki da cin hancin Najeryia duk hira ce – Sule Lamido
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana tababa a kan yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari a cewarsa batun duk hira ce don shi kan sa jagoran gwamnati na da tabon rashawa
A ganin sa yaki da cin hancin da gwamnatin APC ke yi, ya fi karkata a kan jami’an gwamnatin PDP ne,ya bukaci shugabanni su rika fada wa mabiyansu gaskiya, maimakon biye wa son rai a kan rashin gaskiya ba Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana tababa a kan yakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ke cewa tana yi na cin hanci da rashawa.
Lokacin da ya yi aiki a gwamnatin Janar Sani Abacha. “A wancan lokacin dai ya yi aiki da Abacha. Kuma shi ne na kusa-kusa da shi.
“Abubuwan da ake fada kan batun tsaro da rashawa, ina ganin gaskiyar maganar ita ce Shugaba Muhammadu Buhari yana yi ne a kan matsayin hira. Ba don gaskiya ba.” Kusoshin jam’iyyar adawa ta PDP irinsu Lamido na ganin yaki da cin hancin da gwamnatin APC ke yi, ya fi karkata a kan jami’an gwamnatin PDP wadda ta yi shekara 16 tana mulki a kasar.
Sule Lamido wanda yake a matsayin beli kan tuhumar cin hanci da hukumar EFCC ke yi masa a gaban kotu, ya ce akwai rainin hankali kan yadda ake cewa an bankado makudan kudi amma ba a san mai su ba.
“Akwai rainin hankali a cewa hukumar EFCC ta je wani gida a Legas ta binciko kudi. Shin wa ya ba ta labarin wannan gidan? Ai akwai shi! Kuma mai bada labarin wa ya ce ya mallaki kudin?” Ya ce zancen kawai ne a ce hukumar leken asiri ta kasa NIA ta rasa inda za ta ajiye kudinta sai ta kai su wani gida can a Legas.
Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, ya bukaci shugabanni su rika fada wa mabiyansu gaskiya, maimakon biye wa son rai a kan rashin gaskiya ba. “Muddin za ka nemi mukami a Najeriya, ka neme shi a kan matsayin hankali, a kan hujjar gina kasa da yanayin shugabanci a duniya. Kada yanayin haukan kasa ya firgata ka, ka biye masa”, in ji Lamido.
A cewarsa kamata yi a ce “muna da karfin zuciya da karfin imanin da ke sa wa, mu tsaya a kan gaskiya, ko da ‘ya’yanmu za su ce ba su yarda ba.
The post MAGANAR YAKI DA CIN HANCI DUK TA TSUNIYA CE-INJI SULE LAMIDO appeared first on MUJALLARMU.