Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

BA SANI BA SABO INJI SHUGABA MUH’D BUHARI

$
0
0

shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir David Lawal tare da shugaban Hukumar NIA mai leken asiri bisa wasu zargi dabam-dabam. Tuni aka nada kwamiti domin binciken su Mr. Babachir David Lawal inda mataimakin shugaban kasa zai jagoranta kuma har an soma aiki. Yanzu haka dai Kwamitin ta tattara sunayen wadanda ake bukatar a gurfanar domin samun karin bayani.

Har dai Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu tun kwanaki inda aka dauki lokaci ana masa tambayoyi. An dai bayyana cewa a boye za a yi binciken ba tare da kowa ya ji ba. Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa dai za ayi adalci wajen binciken kuma babu daga kafa ko kadan. A baya dai Hukumar NLC ta bayyana cewa bai dace ace mataimakin shugaban kasa bane zai binciki sakataren Gwamnatin.

The post BA SANI BA SABO INJI SHUGABA MUH’D BUHARI appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>