Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
25-4-2017
Duk cewa, Ruwa su ne sinadari na farko da duk wata halitta take so domin rayuwa. An wayi gari talakawan jahar Zamfara, muna matukar shan wahala wajen samun ruwan tare da shan Ruwa marar tsafta, Musamman a garin Gusau da ke zama shalkwatar jahar Zamfara.
Domin yanzu haka, Akan samu Ruwa, na kasa da awanni biyu ne kacal! A kullum. Haka zalika mafiya yawan fanfonan da kan kawo Ruwan sun dena kawo ruwan, Saboda karancin ruwan. Dan haka yanzu mutane kan girgine magudanun Ruwa ne, cikin kwatoci Suna samun ruwan, Duk da Alhamdulillahi sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakkiya, ya yunkuro domin taimakawa wajen gyara wadannan wurare ta yadda za a samu Ruwa masu Tsabta. Amma sai dai kash! Yanzu kusan in ce ruwan sun koma in Yau sun zo to gobe ba su zuwa.
Wanda yanzu haka shekaranjiya ba a kawo ruwan ba Yau ma haka. Duk da cewa gwamnatin jahar Zamfara ta ware maguddan kudade domin gyaran wannan matsala sai dai har yanzu ba mu gani a kasa ba. Dan haka muna Kira ga ita gwamnatin Dan Allah ta kara sanya ido a wannan matsalar. Domin irin yadda ake samo Ruwa yanzu na daya daga cikin ababen da kan kawo, barkewar zabo da amai, malaria da sauran cutukka matara kama da haka.
Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau.
25-4-2017
The post RUWA SUN ZAMA TAMKAR ZINARI A GARIN GUSAU. appeared first on MUJALLARMU.