Bamu Da Tabbacin Ranar Da Zamu Kammala Aiki Akan Kasafin Kudin 2017 – Majalisa
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Toh sai dai rahotannin da suke fitowa daga majalisar a yau na nuna cewa ta sauya shawara saboda ba ta kammala aiki akan kasafin kudin ba.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, sanata Sabi Abdullahi ya shaidawa manema labarai cewa ba shi da tabbacin ranar da za a zartar da kasafin kudin.
Sai dai ya ce kwamitin, a karkashin shugabancin sanata Danjuma Goje ya na aiki tukuru wajen ganin ya kammala aiki akan kasafin kudin, kuma da zarar sun gama za su su gabatar da shi.
Idan mai karatu bai manta ba, sanata Danjuma Goje ya yi ikirarin cewa ‘yan sanda sun kwashe takardun kasafin kudin a yayin da suka kai sumame gidan sa a ‘yan kwanakin baya da suka gabata, batun da ‘yan sanda suka musanta.
Dama dai an tsawaita zangon kasafin kudin 2016 ne zuwa ranar 5 ga watan nan, da tunanin cewa majalisar zata zartar da na 2017 a ranar.
Sanata Sabi ya ce suna sane da wannan, kuma su na iya kokarinsu, domin idan ba a yi ayyuka ba, abun su ma ya shafe su.
The post BAMU DA TABBACIN RANAR DA ZAMU KAMMALA KASAFIN KUDIN 2017-MAJALISAR DATTAWA appeared first on MUJALLARMU.