Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

YAN MAJALISA SUNA CI GABA DA BATA RAWARSU WAJEN YAN NAJERIYA

$
0
0

Kamal Saidu Dansadau

A NAJERIYA har yanzu muna cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki domin har yanzu kayan abinci na nan da tsada kuma akwai karancin aikin yi da jarin fara sana’a.
Wadannan matsalolin na daga cikin irin abubuwan da shugaba Buhari ke kokarin ganin an magance su musamman a wannan shekarar inda yayi kokarin ware wasu kudade domin magance wannan matsala.
Ganin irin matsalolin da talakawa ke ciki a kasar nan baisa Yan majalisa sunyi saura dawowa shugaba Buhari kasafin kudin bana ba, sai dai karin bata lokaci da sukeyi.
Toh Alhamdulillah talakawan NAJERIYA idon su ya bude sossai kuma sun fahimci yan siyasar da ke son su da ci gaba da masu son ganin su a matsala. Kuma da dama sun nuna bacin ransu suna masu sanar da musamman yan Majalisun su wadanda sune wakilansu cewa suna jiraye dasu zuwa zabe mai zuwa 2019.

Dan haka ina kira ga duk dan Majalisan da yasa yana tareda da shugaba Buhari wajen ganin an samu ci gaba a Najeriya ya fito filli ya bayyana kansa dan ina ganin a zabe mai zuwa Zaayi wa yan Majalisa bugu daya ne kuma duk wanda baya tare da shugaba Buhari zai sha mamakin talakawa.

The post YAN MAJALISA SUNA CI GABA DA BATA RAWARSU WAJEN YAN NAJERIYA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050