Abubuwa guda 5 da Osinbajo yayi tun bayan karbar ragamar mulki daga Buhari.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya karbi ragamar mulki -Osinbajo ya fara gudanar da muhimman ayyukan bayan tafiyar shugaban Buhari A daren Lahadi 7 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi balaguro zuwa kasar Ingila, domin samun kulawa ga lafiyarsa, sa’annan Buhari yace bai san ranar da zai dawo ba, sai yadda likitocin sa suka fada bayyana.
Don haka ne shugaba Buhari ya mika mulkin kasar nan ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda hakan ya sanya shi zama mukaddashin shugaban kasa.
Sa’annan shi kansa Buhari ya amince da mataimakin nasa, kuma ya gamsu da nagartarsa da kwarewarsa na tafiyar da gwamnati yadda ya kamata.
Dandalin Mujallarmu.com ta dauko wasu muhimman ayyukan 5 da yayi. Abubuwa guda 5 da Osinbajo yayi tun bayan karbar ragamar mulki daga Buhari Osinba da Buhari
1. Ya jagoranci taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa na tattauna batutuwan kasuwanci a duk bayan watanni uku daya gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa a ranar Litinin 8 ga watan Mayu.
Osinbajo Taron ya samu halartan ministan kasuwanci Okechukwu Enelaman, ministan kudi, Kemi Adeosun, ministan kasafin kudi Udo Udo Udoma da ministan watsa labaru Lai Muhammed.
2. Ya karbi bakoncin tawagar gwamnatin jihar Borno a karkashin jagorancin gwamnan jihar Kashim Shettima da suka kawo ziyarar godiya ga shugaban kasa sanadiyyar ceto yan matan Chibok 82. Osinbajo tare da tawagar gwamnatin jihar Borno
3.A ranar Litinin 8 ga watan Mayu ya karbi bakoncin jakadan kasar Isra’ila Guy Feldman, da mataimakinsa Nadav D Goren a ofishinsa.Osinbajo tare da jakadun kasar Israila
4. Ya taya zabebben shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron samun nasara a zaben shugaban kasar daya lashe. Zababben shugaban kasar Faransa, Macron
5. Ya jagoranci taron kwamitin samar da cigaba a yankin Neja Delta a ranar Talata 9 ga watan Mayu, taron ya samu halartar ministan Ilimi Adamu Adamu da wakilan gwamnatocin jihohin yankin.
The post KARANTA KAJI: ABUBUWA GUDA BIYAR DA MUKADDASHIN SHUGABAN YAYI TUN KAFIN TAFIYAR BUHARI LANDAN appeared first on MUJALLARMU.