Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KALLI HOTUN AHMED MUSA TARE DA AMARYAR SA JULIET EDEH DAYA AURA BAYAN YA SAKI JAMILA

$
0
0

Dan Wasan Kwallon Kafa Na  Nijeriya Ahmed Musa Ya Aure Juliet Edeh

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Dan wasan Leicester City kuma mataimakin kaftin din kungiyar Super Eagles Ahmad Musa ya kara angwancewa bayan da ya saki matar shi Jamila, ‘yan watannin da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa matar da Ahmed ya aura mai suna Juliet Edeh ita ce musabbabin rabuwar shi da matar shi ta fari, kuma uwa ga ‘yayan shi biyu.

An ce an yi ta samun rikici tsakanin dan wasan da uwar ‘ya’yan shi a sakamakon soyayyar da yake yi da Juliet wanda baya boye wa, har ta kai ga ya sanya hoton ta a shafin sa na Instagram, inda ya kira ta sarauniyar shi.

 

Wannan shi ya haifar da rikici na karshe da ya faru tsakanin ma’auratan, wanda har sai da Ahmed ya shafe awanni a ofishin ‘yan sandan Birtaniya akan tuhumar dukan tsohuwar matar ta shi Jamila.

Jim kadan da faruwar haka ne ya yi mata saki uku.

An daura auren Ahmed da Juliet a wata kotu da ke Abuja.

The post KALLI HOTUN AHMED MUSA TARE DA AMARYAR SA JULIET EDEH DAYA AURA BAYAN YA SAKI JAMILA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>