Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA GWAMNATIN TARAYYA TAKI SAKIN SAMBO DASUKI DA IBRAHIM EL’ZAKZAKY

$
0
0

Dalilan kin sakin Dasuki da El-Zakzaki – Inji gwamnatin tarayya.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan da yasa suka ci gaba da tsare Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da Ibrahim El- Zakzaky a gidan yari Gwamnati ta ce tana ba El- Zakzaky kariya daga barazanar dake iya tashi sakamakon samun ‘yanci, shi kuma Dasuki na da jerin shari’un da gwamnati

Malam Garba Shehu ya ce za a amince da ‘yancin Dasuki idan har an kai ga kammala daukacin shari’un da ke gabansa A karon farko tun bayan garkamesu a gidan yari ba tare da beli ba, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilan ci gaba da tsare tsohon mashawarcin tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya da shugaban ‘yan Shi’a Ibrahim El-Zakzaky.
Gwamnatin tarayya ta ce bata da niyayr musgunawa El-Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a birnin Abuja.
 Mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya ce za a amince da ‘yancin Dasuki ne kawai in har an kai ga kammala daukacin shari’un da ke gabansa a halin yanzu.
kotunan Najeriya dama na wajen kasar da suka hada da ita kanta kotun yankin yammacin Africa sun nemi sakin na Kanal Dasuki da ake zargi da almubazzaranci da kudin yaki da ta’addanci kusan dala Amueka biliyon 2.5.

The post KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA GWAMNATIN TARAYYA TAKI SAKIN SAMBO DASUKI DA IBRAHIM EL’ZAKZAKY appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050