Babu Wani Wani Kwamanda Da Zai Iya Yiwa Shugaba Buhari Juyin Mulki -Rundunar Sojin Nijeriya.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Sojin Nijeriya ta bayyana cewa al-umman Nijeriya suyi watsi da jita jitan da ake yi na yunkurin juyin mulkin da wasu ke cewa an yi a kasa.
Hakan ya biyo bayan bayanin da Kakakin rundunar sojin Nijeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka a wani taron da ya yi da manema labarai, inda yake cewa jami’an sojin kasar masu biyayya ne ga dokokin kasar, ba su da niyar yi wa Dimokaradiya da mulkin kasar karan tsaye ko juyin mulki.
Sojojin Nijeriya sun ta’allaka ne ga yin biyayya ga shugaban kasa kuma kwamandan sojoji da tsarin mulkin kasa a cewar Janar Kukasheka kuma rundunar Sojin ta bukaci ‘Yan Nijeriya su kwantar da hankalinsu domin babu batun karbar mulki ta hanyar karfi.
Wannan dai na zuwa a yayin da fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da abin da rundunar sojin kasar ta bayyana kan yunkurin juyin mulkin.
The post BABU WANI YUNKURIN YIWA SHUGABA BUHARI JUYIN MULKI-Inji Burutai appeared first on MUJALLARMU.