Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA WANI MALAMIN MAKARANTA SHIGA KUNGIYAR BOKO HARAM

$
0
0

Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Boko Haram – Malamin Makaranta

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

                   Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Boko Haram – Malamin Makaranta

Wani tubabben dan Boko Haram Ibrahim Suleiman, wanda malamin makaranta ne mai koyar da harshen larabci ya bayyana dalilin da yasa ya shiga kungiyar ta’addancin.

Yayin da yake bayyana kudirin shi na barin kungiyar a jiya Laraba, Sulaiman ya shaida wa manema labarai cewa dama ya shiga kugiyar ne domin ya ceto ‘yayan shi uku, wadanda aka tilastawa shiga kungiyar.

Ya ce ya mika kan shi ne ga rundunar sojin Nijeriya bayan da ya tsira daga dajin Sambisa da shi da ‘yayan na shi uku.

Da yake bayar da labarin sa, Sulaiman ya fadi cewa dan uwansa dan boko haram ne ya kwashi ‘yayan uku masu shekaru tsakanin 4 da goma ya gudu da su dajin Sambisa.

Ya ce a lokacin ya na zaune da danuwan na shi a Yobe, bayan da suka rabu da matar shi wadda suka zauna da ita a Kano.

Ya ce kafin komawarsa Yobe, ya na koyar da harshen larabci kuma ya na dan kasuwancin sa a Kano.

 

A fadar sa “Da uwan nawa ya taba zama da ni a Kano har na tsahon shekara 1, a wani lokaci da sojoji suka tarwatsa su daga Maiduguri”

Ya ce da dan uwan nasa ya gudu da ‘yayan nasa, sai da aka yi watanni 10 kafin ya ji daga gare shi. Da ya tambaye shi dalilin da ya sa ya tafi da ‘ya’yan shi ba tare da sanayyar shi ba, sai ya ce masa ‘ya’yan su na Sambisa su na aikin Allah.

Ya ce dama ya dade da sanin cewa dan uwan na shi dan Boko Haram ne, amma bai taba sanin zai iya kwashe masa ‘ya’ya ya saka su a kungiyar ba.

“Na yi iya kokarin ganin dan uwanan ya dawo min da ‘ya’yana amma abun ya caskara, lamarin da ya sa na yanke hukuncin shiga kungiyar domin na ceto su da kaina”

Ya ce da ya kira dan uwanshi ya fada masa cewa zai shiga kungiyar, ya cika da farin ciki. Ya ce ba tare da bata lokaci ba ya fada ma shi idan zai zo su hadu a Maiduguri, daga nan suka tafi dajin Sambisa.

Ya ce sun wuce sansanonin ‘yan Boko Haram fiye da 30 kafin su isa sansanin Kandahar, inda a nan ne aka ajiye shi.

“Da aka tambaye ni mai zan yi, sai na ce zan koyar da harshen larabci, a lokacin ne na fuskanci cewa zai yi wuya na iya fita daga dajin nan, sai na mayar da hankali na.”

Ya ce tunda ya shiga kugiyar bai taba ko daukan makami ba balle ya zubar da jini, amma an sha kashe mutane a gaban shi.

Ya ce ayyukan kungiyar Boko Haram cike suke da jahilci da rashin imani kuma sun yi hannun riga da koyar war addinin musulunci.

Bayan rikicin da ya faru tsakanin Maman Nur da Shekau ne ya ce ya dauki ‘ya’yan ya bi bangaren Mamman Nur.

Ya ce rashin imanin Shekau ga yara da mata da tsofaffi ne ya haifar da rikicin.

“A lokacin da sojoji suka far wa sansanin da ke kan iyakar Chad ne na iya guduwa da ‘ya’yana, yayin da danuwa na da sauran ‘yan kungiyar suka rasa rayukan su.

Ya ce ‘yan Boko Haram shaidanu ne marasa imani. Su na shaye shaye, suna yi wa mata fyade kuma su na kashe mutanen babu gaira babu dalili. Ya ce su na yi wa talakawa sata, su kuma hora mambobin su da yunwa, a don haka duk abunda suke yi ya saba wa koyarwar musulunci.

The post KARANTA KAJI: DALILIN DAYASA WANI MALAMIN MAKARANTA SHIGA KUNGIYAR BOKO HARAM appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>