Fitacciyar jarumar fina finan Hausan nan, kuma mai baiwa gwamnan jahar Kano shawara kan harkokin mata, wato Rashida Adamu wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a ta zama shugabar matan kungiyar matasan jam’iyyar APC na yankin Arewa da ya kunshi jahohi 19.
Jarumar ta yi nasarar samun matsayin ne a wani taro da jam’iyyar ta gudanar a garin Kaduna, bayan da ta kada abokan takararta mata guda takwas.
Baya ga wadannan mukamai, Rashida ita ce shugabar mata ta kungiyar ‘Social Media’ ta jahar Kano, sannan kuma Jakadiyar Arewacin Nijeriya ta masu shirya finafinai.
Rashida ta bayyana matukar jin dadin ta game da wannan shugabanci da ta samu, ta kuma yi fatan Allah ya taya ta riko.
The post MATSALOLIN DA SA MATSATTSUN WANDUNA KE JEFA WASU ‘YAN MATA appeared first on MUJALLARMU.