Buhari ka gaza – Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
-Babban malamin nan na addinin musulunci, Ahmed Abubakar Gumi, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza ma ‘yan Najeriya
– Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da jam’iyyun APC da PDP baki daya
– Gumi ya bayyana cewa a gwamnatin shugaba Buhari, manyan jami’ai na tafiya da kudaden sata da kuma rashawa Wani babban malamin musulumci Sheikh Ahmad

Abubakar Gumi ya bayyana cewa gwamnatin shugabna kasa Muhammadu Buhari ta gaza sosai. Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayinda yake kimanta gwamnatin shugaban kasa Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai ciki kin shekaru biyu da tayi a kan karagar mulki.
A cewar malamin, shugaban kasar da jam’iyyar sa basu yadda ake zata ba. Malamin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da gwamnati mai ci wato APC da kuma jam’iyyar Peoples Democratic Party.
Sheikh Abubakar Gumi ya kalubalenci shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya gaza ma yan Najeriya Sheikh Gumi ya kuma raina tsarin mulkin jam’iyyar mai ci a yanzu.
Da yake magana a kan cin hanci da rashawa, Gumi ya bayyana cewa ko a gwamnatin shugaba Buhari, manyan jami’ai na satar kudi da rashawa.
The post KUNJI ABINDA BABBAN MALAMIN MUSULUNCI YACE GAME DA SHUGABA BUHARI-(Karanta) appeared first on MUJALLARMU.