Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

WATA MATA TA SAIDA ‘YA YANTA 4 DAGA CIKIN BIYAR 5 BA TARE DA SANIN MJINTA BA

$
0
0

Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba.

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

An kama wata mata a jihar Lagas kan zargin cewa ta sayar da ‘ya’yanta an rahoto cewa matar gidan mai suna Vicky ta sayar da hudu daga cikin ‘ya’yanta biyar sannan kuma ta yi wa mijinta karya.
                   
A sirinta ya tonu ne bayan ta siyar da na karshem kan N400,000 sannan kuma wata makwabciyar ta ta sanar da mijin Jami’an ‘yan sanda sun kama Misis Vicky, wata matar gida a Lagas kan zargin cewa ta sayar da hudu daga cikin ‘ya’yanta biyar ga mutane daban-daban ba tare da sanin mijinta ba.
Mijinta ya aika takarda ga shugaban ‘yan sandan yankin ACP Austines Akika sannan kuma yaba jami’an ‘yan sanda umurnin kama ta.
 A cewar PM Express, tana sayar da yaran ne daya bayan daya sannan kuma ta yi nasaran sayar da hudu daga cikin yaran.
Da farko, ta yi ma mijinta karyan cewa ta kai yaran gurin ‘yan’uwansu ne har sai lokacin da mijin ya gano daga baya cewa tana sayar da yaran ne.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu labarin cewa ta sayar da na karshen a kan N400,000 sannan makwabta suka sanar da mijin wanda ya kai kara gidan ‘yan sanda aka zo aka kamata sannan aka tsare ta a kurkuku.
An rahoto cewa ta rigada ta fada ma ‘yan sanda gaskiya yayinda ake kokarin ceto yaran sannan kuma a kama wadanda suka siya yaran.

The post WATA MATA TA SAIDA ‘YA YANTA 4 DAGA CIKIN BIYAR 5 BA TARE DA SANIN MJINTA BA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>