Jami’an ‘Yan Sanda sun gano gidan makamai a Jihar Benuwe An damke mutane 3 da ake zargi da kera makaman Da alama ba yau aka fara wannan aiki ba
CP Bashir Makama yace dubun masu mummunan laifin ne ya cika a ranar. Da alamu dai an saba kera mugayen makamai a gidan daga nan kuma ake saidawa a sauran wurare. Cikin kayan da aka samu dai har da tukunyar gas da babur da zarto. Kun ji cewa mun samu labari daga kafafe da dama cewa jiya da dare an yi wani mugun fada tsakanin ‘Yan Sanda da Jami’an Sojoji wanda yayi sanadiyar mutuwar ‘Yan Sanda da dama. Majiyar mu tace an fara rikicin ne da Sojojin ruwa daga baya sauran Sojoji su ka kutso ciki.
The post ‘YAN SANDA SUNYI ABUN AZO A GANI appeared first on MUJALLARMU.