A gasar da aka yi a jihar Oyo, a kudancin Najeriya, wata ‘yar karamar yarinya ta lashe gasar zunzurutun kudi har naira miliyan shida a gasar kimiyya ta lissafi, inda ta doke mutum 40 kafin ta cinye gasar, a wata bajinta da aka dade ba’a gani ba a jihar.Yarinyar dai ‘yar talakawa ce kuma ‘yar kauye, amma ta nuna kwazo da hazaka a gasar, ‘yar asalin Fidiki, maraya a cikin jihar Oyo.
Ta lashe kyautar ta gasar kasa baki daya, bayan da ta buge yaran masu kudi daga makarantun masu kudi, kuma taci kyautar kudin har Naira miliyan shida. Ana yawan samun irin wadannan yara dai a Najeriya, sai dai ba safai suke samun tallafi don su zama wasu masu tabukawa kasa komai ba, sai dai alkawurra na siyasa.
The post KUJI YANDA ‘YAR TALAKA TA SAMU KYAUTAR MILIYAN SHIDA (6) appeared first on MUJALLARMU.