Dangote na biyan jihar Binuwe harajin N700,000,000 – Inji Gwamna .
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom yace Dangote na biyan haraji yadda ya kamata Dangote ya rarraba Babura masu kafa uku a Binuwe Gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom ya bayyana cewar kamfanin Dangote dake garin Gboko na biyan harajin naira miliyan 700 ga gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da kamfanin simintin Dangote ya kaddamar da aikin rabon mashin mai kafa uku, da aka fi sani da suna adaidaita sahu a ga wasu al’ummomin jihar Binuwe a satin data gabata.
Dangote ya samu wakilcin mashawarcin sa Joe Makoju a wajen aikin rabon, inda gwamnan jihar tare da mukarrabansa suka halarci taron.
Gwamnan yayin kaddamar da rabon kekunan Gwamna Ortom yayi alkawarin magance duk matsalolin da ake fuskanta musamman a sha’anin karba da biyan kudaden haraji a jihar, inda ya kara da cewa da ba don kamfanin Dangote ba, da bai san halin da tattalin arzikin kasar zata shiga ba.
Daga karshe Dandalin Mujallarmu.com ta ruwaito gwamnan na yaba ma kamfanin Dangote saboda samar da ayyukan yi ga matasan jihar, da kuma gudanar da ayyukan jin kai don amfanin al’ummar jihar.
Sauran aikace aikace da aka kaddamar sun hada da samar da wuta a kauyen Masaje, Ipav, Gaando, Mbayion, Igyula, Amua da Tsekutsa. Sa’annan an kaddamar da gina azuzuwa 14 a kauyukan.
The post KARANTA KAJI: YADDA DANGOTE KE BIYAN NAIRA MILIYAN 700,000,000 A MATSAYIN KUDIN HARAJI A JIHAR BENUWE-Inji Gwamna appeared first on MUJALLARMU.