Takaitaccen Jaruma Hadiza Gobon
Marubuci;Haruna Sp Dansadau

Hadiza Gabon ta yi karatun firamare da sakandirenta a mahaifarta (Libreville) inda bayan ta kammala da kyakkyawan sakamako ta ci gaba da karatu a jami’ a don cika burinta na zama kwararriyar lauya. Sai dai kafin ta kai ga cimma burinta na zama lauya, sai karatun nata ya gamu da tasgaru, inda a dole ta ajiye karatun
Hadiza Gabon ta sake komawa makaranta inda ta yi karatun difloma akan nazarin harshen Faransanci. Bayan ta kammala karatun nata ne ta fara aiki a matsayin malamar harshen Faransanci a wata makaranta mai zaman kanta
Bayan koyarwa na wani dan lokaci, Hadiza Gabon ta bar gida ta dawo Nijeriya, inda ta fara sauka a garin mahaifiyarta wato Adamawa, daga bisani kuma ta koma Kaduna da nufin shiga harkar fina-finan Hausa
A can Kadunan ne ma Hadiza ta gamu da Ali Nuhu wanda shi ne ya taimaka mata wajen shiga harkar fim ka’in da na’in. Hadiza ta fara fitowa a fim din Artabu a shekarar 2009
Jerin Wasu Finafinai da Hadiza Gabon ta taka rawa a cikinsu
-
- Artabu (2009)
- Daina Kuka
- Farar Saka
- Fataken Dare
- Jinin Mijina
- Kolo
- Mukaddari
- Sakayya
- Umarnin Uwa
- Ziyadat
- Wasila (2010)
- Umarnin Uwa(2010)
- Aisha Humaira (2012)
- ‘Yar Maye (2012)
- Badi Ba Rai(2012)
- Akarizziman (2012)
- Dare Daya(2012)
- Wata Tafi wata(2012)
- Da Kai Zan Gana (2013)
- Haske (2013)
- Ban Sani Ba(2013)
- Mai Dalilin Aure (2014)
- Daga Ni Sai Ke (2014)
- Ali Yaga Ali (2014)
- Basaja(2014)
- Daga Ni Sai Ke (2014)
- Uba Da ‘Da (2015)
- Indon Kauye(2015)
- Ba’asi (2015)
- Jarumta(2016)
Nasarorin Da Hadiza Gabon ta samu
Tun bayan sanya kafarta a harkar fim din Hausa, Hadiza ta samu nasarori da dama da suka hada da: Gwarzuwar jarumar shekarar a shekarar 2013 na Best Of Nollywood Awards a fim din Babban Zaure. A wannan shekarar dai, Hadiza Gabon ta samu wani kanbi daga gwamnatin jahar Kano da aka yi wa lakabi Kwankwasiyya Award bisa kokarinta wajen habaka harkar fim a jihar
A shekarar 2014 ma Hadizar ce ta lashe kanbin gwarzuwar shekara na Kannywood MTN Awards karo na biyu a fim din Daga Ni Sai Ke
A shekarar 2015 Gabon ta sake lashe kanbin mataimakiyar babbar jaruma a bikin karrama ‘yan wasa na Kannywood AWA 24 Film & Merit Award a fim din Ali Ya Ga Ali
Ko a bara ma dai sai da Gabon ta sake lashe wani kanbin na gwarzuwar shekara a bikin karrama ‘yan wasa na African Hollywood Awards
Haka kuma, Hukumar Kula Da Makarantun Sakandire ta Jihar Kano sun mika takardar Yabo ga Hadiza Gabon bisa tallafawa harkar ilimi da jarumar ke yi a makaratun jihar
Sai kuma kungiyar Statup Kano da ta mika irin waccan takardar Godiya da Yabawa ga Hadiza Gabon bisa tallafawa masu kananan sana’o’i a jihar Kano
Shekarar 2016, Hadiza Gabon ta kafa wata gidauniyar taimakawa masu karamin karfi da nakasassu da ta yi wa lakabi da HAG Foundation (Gidauniyar Hadiza Aliyu Gabon). Gidauniyar an kafata ne da nufin tallafawa masu ‘yan gudun hijira a harkar ilimi da lafiya. Wannan ya sanya ta zama mutum ta farko a Kannywood da kafa gidauniya da irin wannan manufar
Ko a watan Maris na shekarar da ta gabata sai da Hadiza Gabon ta kai wata ziyarar tallafi sansanin gudun hijira da ke jihar Kano, inda ta bada tallafin kayan abinci da suturu da wasu kayan bukata ga ‘yan gudun hijiran
Hadiza Gabon, jakadiya ce ga kamfanonin MTN Nijeriya da taliyar Indomie
A yau ne wannan bijimar jarumar ke cika shekaru 28 da haihuwa, a saboda haka ne ma mujallar Al’ummata ke taya ta murna da fatan Allah ya ja mata gora.
Allah ya sa ta dade tana yi, amin
The post DANDALIN KANNYWOOD: TAKAITACCEN TARIHIN JARUMA HADIZA ALIYU GABON appeared first on MUJALLARMU.