Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji.
Marubuci:Haruna Sp Dansadau
Babban bankin Najeriya zai fara saidawa jirage Dalar Amurka Haka kuma za a rika saidawa masu jigilar mai da manoma Dalar Babban bankin kasar na cigaba da sakin Daloli a kasuwa Kun ji cewa Dalar Amurka na rage daraja a kasuwar canji Yanzu ma dai Dalar tana kan N366 ne. Hakan dai na nuna cewa abubuwa na dan kara kyau.

Babban bankin Najeriya zai fara saidawa manoma Dala Jiya kun ji cewa bisa dukkan alamu dai ana shirin kai ga ci a tsarin na CBN don kuwa Naira na ta kara tashi sannu a hankali.
Kuma ana sa rai Nairar ta kara daraja nan gaba yayin da CBN ke cigaba da dumbuza Daloli a kasuwa.
Darajar Naira na yin sama a kasuwar canji Yanzu haka dai za a fara saidawa kamfanin jirgin sama Daloli domin a samu sauki.
Haka kuma za a rika saida Dalolin ga ‘yan kasuwa masu harkar mai da kuma manyan manoma kai tsaye. Hakan dai zai yi maganin cunkoson da ake samu wajen neman Dalar. Yanzu dai ana saida Dalar a kasuwar canji ne a kan N366.
Bankuna kuma na saidawa kan 305.60.
A makon jiya an saida Dalar Amurka ne a kan N382.
The post NAIRA TA TASHI: DARAJAR DALA NA CIGABA DA DAKILE WA A KASUWAR CANJI appeared first on MUJALLARMU.