Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

DATTAWAN AREWA SUNYI ALLAH WADAI GA MASU SON A RABA NIJERIYA

$
0
0

              Dattawan Arewa sun yi tur da batun raba kasa

Marubuci:Haruna Sp Dansadau

Dattawan Arewa sun yi Allah wadai da batun raba kasa,Sun ce wannan kiraye-kirayen ba abune da zai haifar da da mai ido ba har ila yau sun ba da shawarar a zauna a tattauna a tsakanin dattawan da ma matasan arewa domin nemo mafita Wasu daga cikin ‘yan Majalisar Dattawa shiyar Arewa, sunyi Allah wadai da wa’adin da kungiyar matasan arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo na su tattara komatsansu su bar yankin na Arewa a cikin watanni uku.

 Da suke sharhi a kan wannan al’amari dattawan arewa sun nuna cewa wannna kiraye-kiraye da ya fara fitowa daga yankin kudu maso gabas, ba abune da zai haifar da da mai ido ba, domin yana iya kawo rabuwar kai d kiyayya mai karfin gaske a kasar.
Madawakin Daura, Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta arewa, ya ce kamata yayi ace duk abin da ake yi a zauna a tattauna a tsakanin manyan arewa da ma matasan domin nemo mafita.
            
 Wannan ne yasa aka kirkiro Majalisar Zartarwa ta gwamnoni da shugaban ‘kasa. Dattawan Arewa sun yi tur da batun raba kasa Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta arewa, ya ce kamata yayi ace duk abin da ake yi a zauna a tattauna a tsakanin manyan arewa da ma matasan domin nemo mafita Sanata Bukar, ya ja hankalin jami’an tsaro da su san irin matakin da zasu ‘dauka, haka zalika gwamnoni da wakilan tarayya da Majalisu su zauna su samar da matsera kan wannan al’amari.
A daya bangaren Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, daga jihar Kano ta Kudu, yayi sharhi a kan al’amarin inda yayi nuni kan cewa zama tare shine mafi alkhairi, saboda cewa dukkan al’umman Najeriya na bukatar junansu.

The post DATTAWAN AREWA SUNYI ALLAH WADAI GA MASU SON A RABA NIJERIYA appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>