Gwamna Dr. Abdulaziz Abubakar Yari ayau 07/06/2017 ya karbi bakuncin Jakadan America W. Stuart Symington agidanshi dake Mafara.
Jekadan na America yace yazone Zamfara domin Ganin yanayin yankin Arewa maso yamma ta Nigeria tareda inganta dangantaka tsakanin Nigeria da kasar America.
W. Symington yace Kasar America zata hada hannu da Nigeria domin inganta shaanin Tattalin arziki da kiwon lafiya da Noma dakuma ilimi.
Dayake Jawabin Godiya Gwamna Yari yace sun tattauna sosai akan cigaban kasar Nigeria da inganta shaanin tsaro.
Hakama Gwamna ya jagoranci tawagar ta jikadan na America zuwa wurin Mahaifiyarshi kasancewar yaga Photonta cikin Falonshi kuma anfadamashi tana nan Raye.
ABUBAKAR S. LIMANCHI
MIN. OF INFORMATION
The post KARANTA KAJI: GWAMNA Dr. ABDULAZIZ YARI YA KARBI BAKUNCIN JAKADAN KASAR AMURIKA appeared first on MUJALLARMU.