Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Najeriya Zata Iya Sayar Da Kaddarorinta Kuma Ta Kasance Tana Gudanar Da Su

$
0
0

Najeriya Zata Iya Sayar Da Kaddarorinta Kuma Ta Kasance Tana Gudanar Da Su

Batun sayarwa ko cefanar da wasu kayayyaki da gwamnatin Najeriya ke shirin yi, na nufin cewa duk kamfanonin ko hukumomin da aka sayar zai koma ne ga hannun ‘yan kasuwa.

A wani karin haske da masani kan tattalin arziki Salihu Garba yayi, yace kasa irin ta Najeria zata iya sayar ka kaddarorinta ta wasu hanyoyi, wanda suka hada da sayarwa ‘yan kasuwa kaso Hamsin ko Saba’in ita kuma ta rike sauran abin da ya rage, yin hakan zai sa ta kasance da hannunta a gudanar da harkokin kamfanin. idan kuma ta sayar da kamfanonin kacokan to hakan na nufin cewa kasar ta cire hannunta daga gudanar da wadannan kamfanonin.

Tsarin tattalin arziki irin na jari hujja ya tanadi cewa idan gwamnati zata sayar da wasu kaddarorinta da kauracewa sayar da su kacokan, domin rana daya za a iya wayar gari aga cewa gwamnatin bata da kaddarori, musamman ma idan gwamnati tayi amfani da kudaden wajen wasu hanyoyi da kudin ba zasu haihu ba ko su kawo wasu kudaden.

Kasar Najeriya dai ta bata sayar da wasu kaddarorinta a baya, missali kamfanin dake samar da wutar lantarki na NEPA da kuma kamfanin sadarwa NITEL, sai dai kuma rahotanni na nunin cewa har yanzu babu wani canji ko ci gaba da aka samu.

 

Daga Dandalinvoa.com

The post Najeriya Zata Iya Sayar Da Kaddarorinta Kuma Ta Kasance Tana Gudanar Da Su appeared first on MUJALLARMU.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>