Power Bank ya wani abu muhimmi ga masu anfani da wayoyin zamani, musamman masu yawan waya da shiga yanar gizo. Mutane da dama suna anfani dashi domin a koda yaushe zasu iya saka wayar su a wuta su samu caji.
Idan zaka sayi Power bank ya kamata ka kula da wadannan abubuwan:
1: Power Output
Power bank bazai amfane ka ba idan har bayada Output da zai iya ya ba wayarka karfin wutar da take bukata ba. misali mafiyawancin wayoyin zamani suna bukatar akalla karfin wuta 2 Ampere suyi caji, dan haka ka tabbatar daga cikin wurin cajin akwai wanda yake da 2.1 a Power bank da zaka saya.
wasu suna kofarin suna caji amma baya shiga saidai suga yana raguwa ba komai bale illa cajin na fita ne daga wayar tasu zuwa power bank din.
2. Battery Cells
Akwai battery Cell kala 2 Li-ion da Li-poly, kuma ko wane su ana anfani dashi ne wajen yin Power Bank masu kyau, mafi yawanci ana anfani da li-ion wajen yin power bank domin kuwa yafi arha, amma Li-poly yafi rike caji kuma bashida matsala wajen anfani kamar li-ion.
3.Power Capacity
Abun na gaba mahimmi shine yawan karfin wuta da zai iya dauka, idan zaka saya ka duba sossai ka tabbatar da zai iya cajin wayarka akalla sau biyu da rabi. misali idan power bank naka da 9000MAH kuma batur na wayarka nada 3000MAH . Power Bank naka zai iya cajin wayar ka sau 2 ne kacal ba sau uku ba. saboda kashi 70 cikin 100 na cajin power bank kadai zaka iya anfani dashi.
Allah sa wannan ya anfani mai karatu. Amin
Mungode da kasancewa tare da Mujallarmu.com
Zaka iya binmu a shafinmu na Twitter: @Mujallarmu
Facebook: dandalin Mujallarmu
Instagram: @mujallarmu
The post Abubuwanda zaka duba kamin ka sayi Power Bank appeared first on MUJALLARMU.