MATSALAR YAWAN FITSARI (Polyuria)!!!
Akwai abubuwa da dama da kan iya kawo yawan fitsari, tun daga canjin yanayi, zuwa yawan shan ruwa ko kayan shaye-shaye, zuwa samun juna biyu zuwa rashin lafiya zuwa magunguna.
Yawan fitsari na faruwa yayin da mutum ya ga cewa yawan zuwa bandakinsa domin fitsari ya karu, ko yawan fitsarin da ke zuba ya karu ko da ba samu karuwar zuwa bayan-gidan ba.
Canjin yanayi daga na zafi zuwa na sanyi zai iya kawo yawan fitsari. Yawa a nan na nufin zubar fitsari mai yawa ba kadan ba.
Yawan shan abubuwa masu ruwa ma kan iya kawo irin wannan yawan. Mai juna biyu ma da ya fara girma za ta rika jin fitsari a kai-akai saboda mahaifa na danno mafitsara.
Sai Rashin lafiya. Ana ganin shigar kwayoyin cuta mafitsara kan iya sa yawan fitsari, amma a nan yawan na nufin yawan jin fitsarin, don ko an je ba a ganin yana zuba da yawa. Wani ciwo mai kawo irin wannan alama kuma shi ne na kumburin prostate a maza wadanda suka manyanta.
Sai matsalar ciwon suga, wadda ita kuma za ta iya kawo yawan yin fitsari a kai-akai, kuma mai yawa ba kadan-kadan ba. Sai matsalar ciwon koda, ita ma za ta iya kawo yawan fitsari kafin daga bisani ya dauke a wasu lokutan.
Daga karshe sai wasu magunguna.
Magungunan da akan ba wasu wadanda ruwa ya taru a jikinsu kamar masu hawan jini misali ko masu ciwon hanta, kan iya sa yawan fitsari. Akwai wasu na gargajiya ma wadanda mutum kan saya ya sha haka nan a titi, su ma za su iya kawo yawan fitsari.
Don haka duk wanda yake da alamomin yawan fitsari ba na canjin yanayi ko na shaye-shaye ba yana da kyau ya je a duba shi, in ta kama ma a yi masa gwaje-gwaje don a tantance matsalar.
WANNAN SHINE JAWABI ATAKAICE!!!
The post MATSALAR YAWAN FITSARI (Polyuria)!!! appeared first on MUJALLARMU.