DARAJAR ‘YA MACE GIDAN MIJIN TA.
“””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””””
A hausance idan muka ce gidan miji, yana nufin aure, Yayin da Aure ke nufin zamantakewar rayuwa marar iyaka tsakanin mace da namiji bayan amincewar su, yardar su, tare da cika sharruda na addini da na al’ada gami da bayyana shaidu da kuma waliyyan ma’auta.
Ita kuma ‘Ya mace wata kyakkyawar halitta ce Wadda Allah ya halitta daga wani yanki na annabi Adam. Hakama Allah ya sanya jagorancin ta a karkashin namiji domin Ya kasance garkuwa agare ta.
Yawon ragaita, Ko bambadanci Sam bai dace da ‘ya mace ba, domin duk yanda ki ke ganin duniya nayi dake, Ko mazaje na ribibinki izuwa Wata harkalla tare da saka ki acikin mu’amalolin su na duniya, daga zarar shekarun tsufa sun tunkaro ki zasu fara ja baya dake daga karshe suyi watsi dake su kuma samo Wata sabuwa ke kuma kin zama tsohon Yayi.sabanin mijinki na aure bazai taba watsi dake ba domin tsufan ki.
Yana daga cikin wadannan dalilai manzon Allah (S. W. A) yace; “Macce tana da sutura kwara biu (rufin asiri) , kabarin ta, Dakuma dakin mijin ta”.
Da Wannan nake Kira ga dukkanin mata musulmi cewa, su sani basuda wata daraja ko kima face ta aure.
Ya Allah kasa ‘yan matan mu da zawarawan mu su gane martabar aure, su kuma shige dadin mazajen su, domin kariya wa martabar su.
Jumma’at Mubarak.
Dan uwanku a musulunci Zayyanu A Maigishiri Gusau.
Director admin matasan Zamfara ta tsakiya.