Daga: Muhammad Bashir Amin
A wata hira da Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi ya gabatar a cikin shirin ‘Bakonmu Na Mako’ Na gidan Talabijin na Liberty TV dake Jihar Kadunan Nijeriya.
Farfesa Angon ya zargi Shugaba Buhari da cusa marasa kwarewa a gwamnatinsa, wanda yake kallon lamarin a matsayin wani abin takaici kuma abinda zai iya gurgunta burin da ake da shi na mayar da Nijeriya cikin hayyacinta, inda ya kama Sunan wasu madafun iko da yake kallon masu rike da madafun cewa tamkar ba’a dora kwarya akan gurbinta ba, daga cikin madafun ikon da ya yi ishara akwai kujerar Sakataren gwamnatin Tarayya da sauransu.
Farfesa ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mai gogewar aiki fa burin samar da ci gaban kasa amma Gwamnatinsa cike take da rauni ta fuskar masu gogewar aikin gwamnati dama a bangaren siyasa.
Ya ci gaba da bayyana cewa Arewa bata ci ribar zabar Buhari ba ta fuskar raba madafun aiko masu maiko da za su kawo wa yankin na Arewa ci gaba cikin sauri.
Ko ya kuke kallon ra’ayin na Farfesa Ango Abdullahin ?
Lahadi: 06/11/2016.