Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Kara Ceto Daya Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

$
0
0

Makonni kadan bayan da aka sako ‘yan matan Chibok guda 21, rundunar Sojin Najeriya ta ce ta sake gano daya daga cikin ‘yanmatan Chibok a garin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza a jahar Borno.

Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya sanar da cewa sun yi nasaran ceto yarinyar mai suna Maryam Ali Maiyanga ne da safiyar ranar Asabar bayan da ta gudu daga dajin Sambisa.

An mika Maryam wadda aka same ta dauke da yaro mai kimanin watanni 10 ga asibiti ba tare da bata lokaci ba domin a duba lafiyarta, Sannan daga bisani aka mika ta ga gwamnatin jahar Borno.

Kwamishinan shari’a na Jahar Barista Shehu Lawan shi ya wakilci gwamnan Borno wajen karbar yarinyar daga hannun kwamandan sojin da ke yaki da Boko Haram Janar Lucky irabor.

Gwamnatin Nijeriya dai ta ce ta na ci gaba da tattaunawa da mayakan Boko Haram don ganin an ceto sauran ‘yan matan na Chibok.

daga alummata.com


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>