Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Abubuwa Guda 11 da Ya Kamata Kowa Ya Sani Game da Marigayi Laftanar Kanar Abu Ali

$
0
0

Mutanen Nijeriya, manya da kanana na ci gaba da jimamin rasuwar jarumin kwamandan sojojin sashe na 272 mai kula da tankokin yaki wato Laftanal kanar Abu Ali wanda ya rasu a ranar juma’ar da ta gabata yayin da mayakan Boko haram suka kai masa farmaki a garin malam Fatori tare da wasu sojoji hudu a gurare daban daban.

Ga Abubuwa guda 10 da ya kamata kowa ya sani game da wannan jajirtaccen soja:

1. Kanar Abu Ali Banufe ne dan asalin jahar Kogi kuma ‘da ga Brigediya janar Abu Ali wanda ya rike mukamin gwamnan Bauchi a lokacin mulkin janar Ibrahim Babangida tsakanin shekarar 1990 zuwa 1992, kuma wanda a yanzu haka shine Etsun garin Bassa Nge da ke jahar Kogi

2. Shekarun sa 36, an haife sa ne a watan Agustan shekarar 1980 a jahar Lagos.

3. Ya bar mata guda daya mai suna Samira da ‘ya ya guda uku.

4. A watan Satumbar shekarar 2015, marigayi kanar Abu Ali ya samu karin girma daga mukamin manjo zuwa mukamin laftanar kanal duk da cewa bai kai matsayin a bashi wannan mukami ba, ya samu karin girman ne a sakamakon namijin kokari, da jarumtar da ya nuna a wasu hare hare da rundunar ta kaiwa mayakan Boko haram.

5. Shi ya ja ragamar rundunar da ta karbo garin Baga, Gamboru Ngala, Mungonu da sauran garuruwa daga hannun mayakan Boko Haram.

6. Ana yi masa lakani da Sarkin Yaki (lord of War) a sakamkon rashin tsoro da halin jajircewarsa. Duk da cewa ya na da karamin jiki, ‘yan uwansa sojoji da dama na kwatanta shi ne da zaki, dodon mayakan Boko Haram.

7. An yi masa shedar cewa mutum ne mai kamala, mutunta mutane, kirki mai kuma matukar kishin kasar sa, da a ko da yaushe a shirye ya ke ya mutu domin ya ga ta zauna lafiya, sannan kuma ba ya burga.

8. Shi ne matukin tankar yaki kirar T-72 wacce aka yi hasashen ta fi kowacce kira kyan aiki a rewa maso gabashin kasar nan, a don haka ne illar da ke yi wa mayakan Boko Haram a lokaci daya ta fi karfin wanda sojoji guda 300 za su iya yi.

9. Ya samu lambar yabo daga shugaban rundunar sojin Nijeriya na kasancewarsa abun kwatance wajen jarumta, karfin zuciya da iya aiki.

10. Saboda matukar iya shugabancinsa da iya karfafa gwiwar na kasa da shi, da kula da bukatunsu, da shiga gaba a duk inda aka dosa, daya daga cikin sojojin da suke tare ya taba hasashen cewa kanar Abu Ali shi zai zo ya zama shugaban rundunar sojojin Nijeriya a nan gaba.

11. Ya rasu shi ne a ranar juma’a, 4 ga watan Nuwamba 2014 da misalin karfe 10 na dare a garin Malam Fatori da ke jahar Borno.

A fadar kakakin rundunar sojojin Nijeriya Kanar Sani Usman Kuka-sheka, an san sojojin Nijeriya da jarumta, amma jarumtar laftanar kanar Abu Ali ta Daban ce, wanda idan ana batun jarumta aka kai ga shi, toh babu sauran magana.

Za’a binne sa a yau a makabartar kasa da ke babban birnin tarayya Abuja a misalin karfe 5 na yamma.

Allah ya ji kansa da rahama, ya sa jarumtarsa ta zam abar koyo ga ‘yan baya. Allah ya biya sa da gidan Aljannah, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashi, idan ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da imani.

alummata.com


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>