Na: Danladi Z. Haruna
Al’amarin rayuwa wani lokaci ya kan zo wa dan adam da fadi tashi. Shi ya sa masu iya magana ‘ba kullum ake kwana a gado ba. Wannan haka yake gare ni musamman abin da ya faru da ni a wannan rana da na ambace da suna Bakar Rana.
A nawa ganin, tilas ce ta sa na kira ranar da bakakirin, domin ita ce ranar da ba shiri na shiga kwatami mai doyin gaske. Kuma duk shirina na a wannan yinin bai samu nasara ba. Allah ne kadai ya tarfawa garina nono da yanzu ba sunana Kwamfuturola Ahmed Sufyan ba.
Yadda abin ya faru kuwa, a wannan ranar tun bayan sallar asuba ban koma barci yadda na saba ba, kai tsaye na daura takalmana shafale na fita gudu domin motsa jiki. Sati guda ke nan ina irin wannan fita. Ba komai ya sa haka ba, sai domin na saba da gudu tun kafin zuwan ranar da za a yi mana jarrabawar gudu a hukumar shiga da fici da na mika takarduna na neman aiki.
A hukumance dai ba a ambaci ranar da za a yi wannan jarrabawar ba. To amma an shaida mana cewar ko da takardunka sun cika daidai yadda ake so, wajibi ne sai ka yi nasara a gudun fanfalaki na tsawon kilomita dari da goma. Wannan irin gudu shi masana abin ke kira ‘marathon’. Tuni wani ya tsegunta min cewa na samu hayewa na abin da ake bukata a takarda. Ya rage saura gudu kadai wanda ake ta jira a sa ranar da za a fafata.
Yayin da na isa filin da nake motsa jiki sai na soma da tsalle – tsalle domin na jikina ya dumama kafin na soma gudun da zan iya. Na rika tsalle ina lankwasa gabobina zuwa wani lokaci sannan na soma gudu sannu – sannu.
Na zagaya filin sau biyu zuwa uku sannan na mike dogon titin unguwarmu har karshensa sannan na fada wani lungu mai matsi. Dalilin da ya sa na zabi na rika bin kanana da manyan lunguna, saboda an ce da mu ana iya bi da mu da kowacce irin hanya aka ga dama. To shi wannna lungun da na bi, wani irin matsatsi gare shi ga kuma duhu ko da rana ballantanaa dare. Wani lokacin ma idan ba ka lura ba, kana iya karo da mai tahowa. Sannan ga wata doguwar kwata mai zurfi da ta ratsa tsakiyar layin. Daga karshen layin kuma watau farkon kwatar, nan mutane ke zubar da shara. Hakanan ko’ina kashi ne birjik, kasancewar gidaje sun juyawa lungun baya. Wannan ya sa kusan kullum baya rabo da tashin wari da hamami wani sa’in ma samami da doyi. Ina so na jure da irin wahalar da ake fuskanta a wannan lungun yadda zan saba da kowacce irin wahala idan lokacin gudun ya zo.
Haka kuma, na ji an ce wai ba gudi kadai ake tika ba, an ce Na ji ance ba gudu kadai ake tika ba, an ce ana watsawa mutane wani irin gas yayin da suke gudun. Idan masu gudun suka shaka, sai kuzarinsu ya ragu, idan kuma suka dauke numfashinsu nan ma cutuwa ce. An ce wurin da ake fesawar baya wuce mita biyar. Mai kawo min tsegumi ya shawarce ni da na rika ba wa kaina horon saba wa da wari ko doyi, sannan na koyi dabarar rike numfashi akalla minti biyar alhali ina tikar gudu. Idan na biyo wannan lungun horon da nake yi kenan. To amma fa wani zubin na kan yi kicibis da karnuka suna kale a bola, su yi ta zabga min haushi wanda ke matukar razana ni.
A kowanne lokaci ina tare da mataimakiyata ta musamman, watau wayata. Ban yarda na ajiyeta ko na kashe ba, saboda kusan koyaushe da ita na dogara. A horon gudun nan ma tana cikin aljihuna. Iphone ce mai lamba biyar, watau Iphone 5, kusan komai da ita na ta’allaka. Lambar bankina da email, da alkawarurruka kai har da kwafin dukkan takarduna na ciki.
Ina cikin gudu a lungun na tsayar shakar iska domin fatan sabawa da hakan kafin ranar gudun gasken wayar tawa tayi kara, alamun shigowar sabon sako. Na ciro ta daga aljihuna na duba. Sanar min yau ce ranar gudun nan za a fara da misalin karfe bakwai na safe. Cikin sauri na duba agogon wayar, shida da mintuna ashirin da biyar. Kenan lokacina ba shi da yawa muddin ina son isa akan kari. Na duba tarihin turo sakon, ashe tun shekaranjiya aka aiko da shi bai zo ba sai yanzu. Ko me ya zaunar da shi haka a hanya? Oho!
Juyawar da zan yi ke da wuya, wayar ta subuce ta fadi kasa. Na kai mata raruma, ta zame sai kuwa ta afka cikin kwatamin nan zundum!
Bakin ciki da takaici ba sai an fada ba, ga dai bani da isasshen lokaci, kuma a gaskiya ba zan iya tafiya na bar wayar nan ba. Idan ma na je babu ita ai na yi zuwan kare ga aboki ne kawai. Akwai lambar takardar neman aiki da ake bukata ka fada, ni kuwa ban rike tawa ba tana cikin wayar. Na yi shiru ina tunanin yadda zan yi.
Alhamis: 10/11/2016.