Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

DAN ALLAH MU GUJI WANNAN LABARIN KARYA GAME DA FURUCIN DA AKACE BURUTAI YAYI AKAN SHUGABA BUHARI

$
0
0

Wannan Labarin karya ne wasu mutane ke kokarin ganin sunyi anfani da wannan dama domin batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Labarin yazo ne kamar Haka:

“Buratai ya zargi Buhari a kan mutuwar Kanar Ali, ya kuma yabi Goodluck

Laftanar Kanal Abu-Ali dai ya mutu. Allah Ya ji kansa da rahama. Amma shin da za mu iya hana mutuwarsa? Kwarai za mu iya!

Janar Buratai, shugaban sojojin Najeriya ya bayyana wasu dalilai da suka haddasa mutuwarsa.

Har wala yau, Buratai ya bayyana dalilan da suka sanya Sojojin Najeriya ke mutuwa a fadan da suke yi da ‘yan Boko Haram.

Ga dai fasa kwan da Buratai ya yi: Lokuta da dama Buhari ya yi ta nuna tsanar sa a kan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

Bisa wannan dalilin ne ya sanya aka sa wa matar tsohon Shugaban kasar ido, ake kuma tuhumar ta.

Shin su Jonathan waliyyai ne? A’a! Shin su Yar ‘Adua, Obasanjo, Ibrahim Babangida da Abdussalami duk waliyyai ne? A’a!

Saboda haka, Janar Buratai ya ce abin ya ishe shi haka. Ya bayyana abin da ke cikin zuciyarsa dangane da kisan kare dangi da ake yi wa sojojinsa.

Kamar yadda Janar Buratai ya fada, tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya samar da makaman yaki wadanda za a iya amfani da su daga nesa.

Kari a kan haka kuma, ya yi hayar wasu sojan haya daga kasar Afrika ta Kudu da makamai na zamani domin su taya shi yaki da ‘yan Boko Haram.

Wannan na daga cikin nasarorin da aka samu cikin kwanaki kalilan a 2015, a cewar Janar Buratai.

Yayin da Buhari ya kasance masani a fannin tsaro fiye da Jonathan, Buratai ya ce abin da ya kamata Shugaban kasar ya yi shi ne dorawa a kan aikin na Goodluck Jonathan, da an yi hakan da tuni Boko Haram ta zama labari.

“Maganar gaskiya shi ne daga watan Satumba zuwa Nuwambar wannan shekara, mun rasa sojojin da ba za su lissafu ba.

” Shahararru daga cikin wadanda muka rasa, akwai Manjo DS Erasmus da sojoji guda 8 – ranar 25 ga watan Satumba 2016 yayin da aka yi musu kwanton bauna da bamabaman kan hanya, wato IED a wajen garin Bama – Hanyar Banki.

“Laftanar Kanal K. Yusuf da sojoji 83 sun bace bat a ranar 16 ga watan Oktoba 2016 lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji a Gashigar.

“An kashe Laftanar Kanal Abu-Ali tare da sojoji guda 5 ranar 4 ga Nuwamba 2016 a hanyar su ta kai dauki ga sojoji a Mallam Fatori.

“Ranar 5 ga watan Nuwamba 2016, an sake kashe wasu sojojin guda 2 lokacin da ‘yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojoji a Kwada.

“An jikkata wani soja, inda aka bayyana batan wasu guda biyu kuma a lokacin fafatawar.

“A wani harin a Kangarwa ranar 6 ga Nuwamba, an sake kashe wani soja yayin da aka ji wa wasu 4 rauni a lokacin fafatawar.

“Goodluck Jonathan ya sayo tankokin yaki samfurin Vickers MBT, tankokin yaki T-72 da kuma bindigogin Shilka. Wadannan makaman ba karamin fatattakar ‘yan Boko Haram suka yi ba.

“Amma yanzu duk sun tsufa, yayin da kuma shi Shugaban Kasa yana sane ya bar sojojin mu su yi amfani da makaman da suka lalace wajen yakar Boko Haram.

“Babban abin da ya kawo wannan jin jiki ga sojojinmu shi ne halin da sojoji ke ciki na rashin ingantattun makamai.

“Bataliyar sojoji mai mutane 700 suna amfani da gilashin hange guda biyu. Biyu kacal! Bayan haka kuma, bataliyar ana raba ta kusan gida biyu ne.

“Wasu bataliyar suna da sojoji 400 ne kawai. Ta ya za su iya kare jure gumurzu da dandazon ‘yan Boko Haram?

“A tuna cewa soja fa babu kayan aiki babu abin da zai iya, sannan kayan aiki babu mutum lallai kusan ba su da amfani ne kawai.

“Wannan ya nuna cewa akwai bukatar ingantattun kayan aiki domin rage yawan mutuwar sojoji yayin fafatawa.

“Abin da muka fi dogara da su sune bindigogin AK 47. Yayin da su kuma ‘yan Boko Haram ke amfani da makaman da sun fi namu.

“Abin takaici, makaman da za su taimaka mana wajen yakin nesa kamar su bindigogin AA, bututun Mortar, manyan makamai kamar bindigogin Shilka da sauran su duk sun yi karanci.

“Yar Nasarar da muka samu a kan ‘yan Boko Haram, ya fara ne a watan Fabrairun 2015 saboda an kawo mana tankokin T-72 wajen fafatawa.

“Har wala yau sojojin kasar Chadi sun taimaka wajen matsin lamba ga ‘yan Boko Haram din a wancan lokacin.

“Amma sai Shugaban kasa ya sallame su baki daya, ba tare da ya wadata sojojinmu da makamai ba. Sai suka gaza.

“Rashin ingantattun makamai, rashin karfin gwiwa, rashin biyan su kudaden su, rashin kara musu girma shi ke sanya ana fatattakar sojojin yayin yakin.

“Lallai Shugaban Kasa ya tashi tsaye ya yi abin da ya kamata,” cewar Buratai.”
Don ganin asalin labarin a duba
Burutai blames Col. Ali’s death on President Buhari, hails Goodluck http://vanguardnigeria.org/burutai-blames-col-alis-death-president-buhari/


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>