Idan mu kayi la,akari da halin da al,ummar jahar zamfara suke ciki musamman ma,aikatan Gwamnati da sauran talakawa jahar zamfara to zamu iya cewa babu wata hubbasa da majalisar tayyi wajen ganin al,ummar jahar sun samu sawaba.
Ma,aikatan Gwamnatin jahar na fama da matsalar Rashin Albashi basu samun albashinsu kan kari, hakama suna fama da matsalar Rashin *Promotion* ga matsalar Rashin samun Karin kudin albashi Yan *fensho* na fama da irin tasu matsalar na rashin samun kudi, hakama tsofaffin ma,aikata masu Jiran Kudin *Garatuti* na fama da irin tasu matsalar, Wanda hakkin majalisar jaha ne ta gayyato Mai Girma Gwamnan jahar domin yaimata cikakken bayanin da yassa wannan matsalar ke faruwa Wanda takici taki cinyewa tun a zangon mulkin farko har izuwa wannan lokaci.
Wace irin kasa wace ta hana yan majalisar mu yin wannan gagarumin aiki Wanda shine silar tsintar Kansu a matsayin wakilan al,umma a zauren majalidar Kodai yana nuna kasawarsu ce wannan jagorancin na al,umma dayake Kansu. Dadama akwai matsalolin da Al,ummar jahar zamfara ke tsintar Kansu a cikinsu musamman matsalar tsaro data addabi, al,ummar jahar Wanda hakkin majalisar jahar ne su gayyato mai Girma Gwamna domin yiwa al,umma cikakken bayani akan wadan nan ababe.
Babu wata rana ko lokacin da majalisar jahar tattaba aika Goron Gayyata ga Gwamnan zamfara akan wani abu da majalisar bata gamsu dashi ba Wanda yashhafi al,umma, Wanda wannan ke nuna cewa ba wakilcin al,umma ne gabansu ba. Da wannan muke kira da babbar murya a madadin kungiyar mu ta matasan zamfara ta tsakiya da yan majalisun mu su gaggauta sanin aikin su inda cen basu sanshi ba. Hakama muna kira ga dukkan yan majalisarmu su sani wakillan alumma suke a majalisa ba wakilcin Kansu sukai ba yakamata susan hakkokan da sunka rataya akansu domin ganin sun saukesu a kowanne fanni na rayuwar al,umma.
Daga Ukhashatu Abubakar Gusau Assistance welfare na kungiyar matasan zamfara ta tsakiya.