A yunkurinta na dakile faduwar farashin Naira a kasuwannin canji, gwamnatin Nijeriya ta umarci jami’an ‘yan sandan farin kaya na DSS da su yi wa ‘yan canji dirar mikiya, sannan su kama duk wanda ke bayarda canji ba akan farashin da aka kayyade ba.
Da yawa daga cikin ‘yan canjin sun shiga hannu tun daga ranar Laraba da jami’an suka fara kamen a jahar Lagos da babban birnin tarayya Abuja.
Al’amarin ya biyo bayan wata ganawa da aka yi tsakanin babban bankin kasa CBN, jami’an SSS da kuma shugabannin ‘yan canji a karshen makon da ya gabata a Abuja.
A ganawar da bangarorin suka yi, sun amince cewa, rashin gaskiyar ‘yan canjin ne ya haifar da faduwar farashin Naira har zuwa N480 kowacce dala a bakar kasuwa duk da cewa ana sayar da ita akan N400 farashin gwamnati.
Sun kuma amince cewa ‘yan canjin za su na fansar Dala daya akan farashin Naira 390 ko kuma kasa da haka, sannan kuma su siyar wa mabukata akan Naira 400 ko kasa da haka.
Gwamnatin Nijeriya dai ta dade tana zargin ‘yan canjin da haddasa hauhawan farashin kudaden waje kamar Dala da Pam da kuma Euro, abin da ke karya darajar Naira.
daga alummata.com