Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

LABARINA: DALILIN DA YASA SAMARI SUKE GUDUNA

$
0
0

Rayuwata ta kasance cike da darasi da abun Lura domin kuwa a wasu shekarun baya na kasance ma’abociya bin Maza muna rayuwa yadda muke so, a lokacin ban taba tunanin cewa lokaci zai zo ba da maza Zasu guje niba, domin kuwa na kasance Kyakykyawa Sannan kuma ina da Surar Mai Kyau. Babu wani Namiji mai Lafiya da zai gannin ba zai ji sha’awata ba.

A gaskiya lokacin na kasance duk Saurayin da yazo mun da Kalmar soyayya bana kula shi face sai na fahimci yana da kudi, sannan kuma idan baka da mota bana ko sauraren ka balle ma in jira in fahimci ko kana da kudi. Wannan yasa Duk wani saurayi da nayi baya taba yadda sai na bashi jikina, dama kuma ni lokacin Rayuwa kawai nake tunani ban taba kawo aure a raina ba. Gani nake duk lokacin da na tashi aure ga Samari nan Zube da suke zuwa wajen ai sai na zaba. Balle ma da dama da nake ba jikin sun bayyana min irin dadina da suke ji idan muka sadu.

Na dade ina irin wannan rayuwar ban farga ba sai ranar da na bukaci kudi wurin Samarina sai naga kowane a cikin su yana nuna min bai da su sai dai in jira wani lokaci, a takaice dai duk sun fara guduna saboda ban saba neman kudi ba in rasa, A duk lokacin da na nema kudi nan take za’a cire a bani.

A halin da ake cikin yanzu saurayi ko daya ba mai zuwa gidan mu kuma, yan anguwar mu da suka nuna suna sona a lokacin da nake cin lokacina duk ko wannen su idan na nuna masa alamun inayi dashi yanzu sai su nuna min ai basuda lokacina. Wannan abun ya matukar sani cikin damuwa domin kuwa ni Yanzu Aure Nake so amma da dukkan Alamu mijin ba zaizo nan kusa ba, koda yazo da yayi dogon bincike toh tabbas yan uwansa ma baza su bari ya aure niba.

Dalilin da yasa na bayyana tarihin Halin da na shiga shine ina Mai ba Yan mata Shawara da su guji irin rayuwar da nayi a baya, domin kuwa Namiji ba dan Goyon Bane musamman irin Yan Iska Masu nema lalata da ‘Yan Mata. Da zarar kika kuskura kika bashi jikin ki toh ki tabbatar ba zai aure ki ba, kuma mafiyawancin samari yanzu basu yarda su aure Budurwar da Ta dade batayi aure ba domin kuwa akwai ‘Yan Mata yara 18-19 Kyawawa da zasu iya aura kinga mai zai sa su kula ki kin shekara 25-28 ba aure. Idan Har Gidan ku baza’a miki aure da wuri ba kila sai kin kai Shekara 20-25 to ki tabbatar da duk wani Saurayi da zakiyi baki bashi jikin ki ba, domin daga nan za’a samu Matsala ki shiga Irin rayuwar da nayo a baya.

Dan Allah ina kira ga Samari da ku dena yaudarar ‘Yan Mata kuna bata musu rayuwa domin kuwa mafi yawanci mu da muka rasa mutuncin mu na ‘ya mace da yaudarar mu ake farawa, dan kowa ce ‘ya mace tana tsoron Ranar farko da ‘da Namiji zai sadu da ita, duk da Yake Wani Lokacin Da son mu hakan take faruwa domin kila tashen Balaga na sa muji Sha’awar Namiji Sossai, Kuma Al’adar Gidan mu sai Mace ta Gama Degree zata yi aure.

Allah yasa mu gyara baki daya, nidai Allah ya shirye ni kuma ina mai ba duk wata ‘ya mace shawara da Wallahi ta bi ahankali da soyayya, domin kuwa daga nan ake fadawa halaka.


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050