Quantcast
Channel: MUJALLARMU
Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050

Shekau Ya Bayyana Ra’ayinsa Game Da Zaben Amurka

$
0
0

Shugaban bangare daya na kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya aika wani sakon murya ga sashen hausa na kafar yada labarai na BBC inda ya bayyana ra’ayinsa game da zaben Amurka.

Haka kuma ya yi amfani da wannan dama wajen daukar alhakin hare haren da ake ta kaiwa a ‘yan kwanakin nan a wasu yankuna a jahar Borno.

A sakon wanda wani na kusa da shi ya tura, Shekau ya bayyana cewa da Hillary Clinton da Donald Trump ba su da wani banbanci, kuma ko da ace Clinton Amurkawa suka zaba, toh sun yi asara.

Ya kara da cewa da shi da mabiyansa a shirye su ke su kalubalanci manufofin zababben shugaban na Amurka.

Haka kuma ya yi Allah wadai da matakin da ya ce sarkin kasar Saudiyya mai bin tsarin shari’ar musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr. Trump.

daga Alummata.com


Viewing all articles
Browse latest Browse all 3050


<script src="https://jsc.adskeeper.com/r/s/rssing.com.1596347.js" async> </script>